Jam’iyyar PDP a jihar Zamfara tace ta karɓi tsohon Gwamnan jihar Abdul’aziz Abubakar Yari da Jama’ar sa.

Shugaban Jamiyyar PDP Bala Mande ne ya sanar da hakan yayin tattaunawa da manema labarai Jim kaɗan bayan kammala wata ganawa ta masu Ruwa da tsaki na Jamiyyar a Gusau.

Dama dai a Ɗan tsakanin nan anata yaɗa jita jitar ficcewar tsohon Gwamnan daga Jam’iyya mai mulki zuwa babbar Jam’iyyar Adawa ta PDP.

Har yazuwa yanzu dai tsohon Gwamnan yana ƙasa mai tsarki Inda yake gudanar da aikin Umra.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here