Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta sanya ranar gudanar da zaben sabbin shugabanninta na shiyyar Arewa maso yamma, biyo bayan gagara da zaben yayi a watannin baya, sakamakon samun rudani a wajen zaben, da ake zargin bukata ce taci karo da bukata tsakanin jagororin jam’iyyar na wannan shiyya, abinda yasa uwar jam’iyyar ta kasa ta kafa kwamitin rikon kwarya, wanda sune zasu jagoranci gudanar da zaben a ranar 28 da watan da muke ciki na Satumba kamar yadda sakataren tsare-tsaren jam’iyyar, Col. Austin Akobundu, ya bayyana.

Jaridar Kano Online News ta rawaito cewa, cikin wata takarda da jam’iyyar ta fitar, mai dauke da bayanin abinda ya shafi zaben, an rubuta sunan shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kano, Alhaji Shehu Wada Sagagi, wanda yake daga tsagin tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ba tare da bayyana sunan Hon. Muhammina Bako Lamido, na tsagin Ambasada Aminu Wali ba, duk kuwa da ikirarin tsagin na cewa sune halattattun shugabannin jam’iyyar PDP a jihar Kano ba tsagin yan Kwankwasiyya ba, abinda a yanzu a iya cewa uwar jam’iyyar bata san shugabancin tsagin Wali ba.

Rabon mukaman shugabancin jam’iyyar PDP na shiyyar Arewa maso yamma, jihar Kano ta samu tagomashin kujerar mataimakin shugaba na yankin, wanda tsagin Kwankwasiyya suka tsaida Muhammad Yusuf Jamo, duk kuwa da cewa Sanata Bello Hayatu Gwarzo yana takarar kujerar, harma yan Kwankwasiyya suka zargi gwamnan Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, da goyon bayan Bello Hayatu domin wata nufaka tasa ta kokarin ganin ya tadiye Kwankwaso, kasancewar sun fito daga shiyya daya, kuma suna da bukata iri daya a jam’iyya daya.

Daga: Kano Online News

13/9/2021

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here