Shugabannin tsaro da ‘yan Majalisar Dattijan Najeriya na ganawa

Shugabannin tsaron Najeriya da na ‘yan Majalisar Dattijan Najeriya na tattaunawar sirri.

Hafsoshin tsaron na amsa gayyatar ‘yan majalisar ce domin bayyana musu halin da ake ciki game da taɓarɓarewar tsaro a faɗin ƙasar.

Babban Hafsan Tsaro, Manjo Janar Leo Irabor ne ya jagoranci hafsoshin tsaron zuwa majalisar, inda Shugaban Majalisa Ahmad Lawan ya karɓe su.

Sauran jamia’n da ke amsa gayyatar sun haɗa da da shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta NIA da kuma na ‘yan sandan DSS.

Bayan Sanata Ahmad Lawan ya gode musu bisa ayyukan kare tsaron ƙasa a madadin majalisar sai suka shiga tattaunawar sirri da misalin ƙarfe 11:21.

Muna tafe da ƙarin bayani da zarar mun samu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here