Gwamnatin Najeriya ta daura alhakin mutanen da aka kashe yayin zanga zangar End SARS kan shugaban kamfanin twitter Jack Doresey.

Ministan watsa labarai na Najeriya Lai Muhammad ya ce Mista Dorsey da kamfanin sada zumuntarsa ne ke da hannu a kisan. Har yanzu ba su mayar da martani kan zargin ba.

Dubban ‘yan Najeriya sun fita kan tituna a watan Oktoban da ya gabata a zanga-zangar adawa da cin zarafin‘ yan sanda.

Ministan yada labarai Lai Mohammed ya yi zargin cewa Mista Dorsey ya kaddamar da gidauniyar hada kudi don gudanar da zanga-zangar, yana neman mutane su ba da gudummawa ta hanyar bada kudin Internet wato Bitcoin.

”Twitter ya kara ruruta wutar rikicin ta hanyar samar da hoton alama dake dauke da tambarin EndSars”, in ji shi.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito Ministan yana cewa “Idan ka nemi mutane su ba da gudummawar kudi ta hanyar Bitcoin don masu zanga-zangar EndSars to lallai za ka dauki alhakin duk abin da sakamakon zanga-zangar ya haifar.”

“Mun manta cewa EndSars ta haifar da asarar rayuka, ciki har da ‘yan sanda 37, sojoji shida, fararen hula 57 yayin da aka lalata dukiya ta biliyoyin nairori.” Inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here