Shugaban Najeriya ya mayar da martani kan matakin gwamnan Ondo na korar makiyaya.

A karon farko, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mayar da martani kan matakin da gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu ya ɗauka na korar makiyaya daga dazukan jihar.

A wani saƙo da mai taimaka wa shugaban ƙasar kan kafofin watsa labarai Malam Garba Shehu ya aika wa manema labarai, ya bayyana cewa fadar shugaban ƙasar na sane da kuma bin abubuwan da ke faruwa musamman kan batun matakin da gwamnan na Ondo ya ɗauka.

A cewarsa, rashin daidaito a irin yadda ake aika saƙo ne yake jawo ce-ce-ku-ce game da ainahin saƙon da ake so a aika wa jama’a.

“Babu wani abin cewa illa kira ga ɓangarorin su yi sulhu da kuma neman gwamnatin jihar da kuma shugabancin Fulani su ci gaba da tattaunawa domin fahimtar juna don kawo ƙarshen rashin tsaron da ake fama da shi a jihar cikin sauri,” in ji shugaban.

Shugaban ya kuma yabi gwamna
Akeredolu inda ya ce a matsayinsa na babban lauya kuma tsohon shugaban ƙungiyar lauyoyi na Najeriya wanda ya yaƙi laifuka cikin shekaru huɗu da ya yi a gwamnan jihar, shugaban ya ce a tunaninsu ba sa tsammanin gwamnan jihar zai kori dubban makiyaya waɗanda suka shafe rayuwarsu a cikin jihar sakamakon wasu ɓata gari suna aikata laifuka a daji.

Shugaba Buhari ya kuma ce idan da gaske ne, lallai ƙungiyoyin kare haƙƙi na kan gaskiyarsu ta nuna damuwa kan cewa wannan matakin kan iya tayar da zaune tsaye.

Ya kuma ƙara jaddada cewa garkuwa da mutane da fashi da makami da satar dabbobi laifi ne kuma ko su wa ke aikata irin laifukan, ya kuma ce bai kamata ana yi wa wata ƙabila kuɗin goro ba ana siffanta ta da wani laifi na musamman.

A makon nan ne dai gwamnan jihar ta Ondo ya bai wa makiyaya da ke dazukan jihar wa’adin kwanaki bakwai su bar dazukan.

Gwamna Akeredolu ya ce a matsayinsa na babban mai kula da sha’anin tsaro na jiharsa, ba zai zura ido ba ya bari ana ci gaba da aikata laifuka.

A cewarsa, sun dauki matakin ne da zummar tabbatar da tsaron rayuka da na kaddarori a jihar ta Ondo yana mai bayar da umarni ga jami’an tsaro su tabbatar da an aiwatar da dukkan umarnin da ya bayar. Bbc hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here