Shugaban kasar Masar AbdelFatah al-Sisi ya kaddamar da hukunin gidaje guda dubu sittin da bakwai da Gwamnatinsa ta gina akan kudi dalar Amurka biliya daga.

Wannan rukunin gidaje sunne cikon gidaje guda miliyan daya da Gwamnatinsa ta gina a cikin shekaru hudu. Gidajen guda miliyan daya sun lashe zunzurutun kudi Dalar Amurka biliyan goma sha biyar.

Shugaban ya sha alwashin kara gina gidaje miliyan daya a kasar cikin kankanin lokaci. Shugaban dai ya samar da sabbin birane yayin da yake gina gidaje da suka kunshi Masallatai na Juma’a da na Khamsu Salawat da filayen wasanni da asibitoci da makarantu da guraren shakatawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here