Shugaba Buhari ya sauke ministoci biyu

Ministoci da Shugaba Buhari ya sauke na Ma’aikatun Lantarki da kuma na Noma

Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke ministoci biyu na ma’aikatun Noma Sabo Nanono da kuma na Lantarki Sale Mamman.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin shugaban Najeriya, Femi Adesina ya fitar a wannan Larabar.

Sanarwar ta ce Ministan Muhalli, Mohammed Abubakar ne zai maye gurbin Ministan Noma, yayinda karamin Ministan ayyuka, Abubakar Aliyu zai maye gurbin Ministan Lantarki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here