Shugaban Kasa Buhari Ya Nada Marubuciyar Littafin Uwargidansa Jakada

Matar da ta wallafa littafi a kan matar Shugaban Kasa, Aisha Buhari ta zama Wakiliyar Najeriya a Hukumar Ilimin Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO).

Shugaba Muhammadu Buhari ya daga likafar Hajo Sani ne mako guda bayan kaddamar da littafin ‘Aisha Buhari: Being Different’, da ta wallafa a kan matarsa, a Fadar Shugaban Kasa.

Kafin nadin nada, Hajo Sani ita ce Mashawarciya ta Musamman ga Shugaban Kasa a kan Harkokin Mata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here