Labari mai dadin ji: Shugaban Jami’ar Yar’aduwa yi wa daliban da suka gaza kammala Jami’ar saboda carryover afuwa

A wani labarin da Katsina Daily Post News ta gani mai dadin ji ga daliban Jami’ar Umaru Musa Yar’aduwa dake Katsina, shugaban Jami’ar Farfesa Sanusi Mamman ya yi afuwa ga wasu daliban Jami’ar da suka gaza amsar sakamakonsu sakamakon yawan carryover da suka samu.

Kamar yadda Aminu Aliyu Tanko ya rawaito mana, ya bayyana cewa;

“Shugaban Jami’ar Umaru Musa Yaradua university dake Katsina Professor Sanusi Mamman ya yi afuwa ga duk wadanda suka gama cinye shekarunsu na degree amma ba su gama ba, da su dawo domin su karasa su amshi sakamakonsu.

Farfesa ya kafa sharudda kamar haka;

1- Dole ne ya zama ba satar amsa suka yi ba aka koresu.

2- Sannan kuma kwasa-kwasan da za su gyara basu wuce goma ba.

3- Duk wanda makinsa CGPA ya gazama 1.50 amma ya kai 1.00 shima ya zo.

Allah yakara azurtamu da jagorori irin Farfesa Sanusi Mamman.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here