Advert
Home Sashen Hausa Shugaban jam'iyyar PDP na jihar katsina ya karɓi 'yan jami'iyyar APC a...

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar katsina ya karɓi ‘yan jami’iyyar APC a malumfashi

MAJIGIRI YA KARƁI ‘YAN JAMI’IYYAR APC ZUWA PDP A MALUMFASHI.

Daga Comrade Mai Iyali

Da safiyar yau Talata jam’iyyar PDP ta karamar hukumar Malumfashi ta yi gangamin amsar Hon.Lawal Yusuf Gangarawa Babban jigo a jam’iyyar APC ta jihar Katsina hade da dubbin magoya bayan shi 2800, Taron wanda aka gudanar a ofishin jam’iyyar PDP na karamar hukumar Malumfashi, Taron ya sami halartar ďimbin al’umma daga Sassa daban- daban na jihar katsina

Shugaban jam’iyyar PDP na shiyyar funtua Hon. Adamu ilyasu Sabuwar kasa ya bayyana shigowar Hon. Lawal Yusuf cikin jam’iyyar PDP a matsayin wata babban nasara ga jam’iyyar, kasancewar sa jajirtacce mutum kuma mai kishin ci gaban al’umma. Kuma ya tabbatar da cewa jam’iyyar ta amshi Hon. Lawal Yusuf da hannu bibiyu ba tare da nuna masa wata wariya ba.

Hon. Lawal Yusuf ya bayyana cewa abin da ya ja hankalinsa har ya yanke shawarar shigowa jam’iyyar PDP shi ne, ganin ýaýan jam’iyyar PDP suna da aķidar taimakon talaka da kuma tausayi da son cigaban al’umma, Sannan Kuma ya yi alkawarin ba da duk kan gudunmuwa don samun nasarar PDP.

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Katsina Hon. Salisu Yusuf Majigiri (Garkuwan Gabas Katsina) shi ne ya miķa katin jam’iyyar PDP ga Hon. Lawal Yusuf amadadin Shugaban mazabar shi, bayan nan ya bayyyana cewa wannan shigowa tashi a PDP Babban nasara ga jam’iyyar PDP kasan cewar shi jajirtacce ne mai son temakon al’umma, Bayan nan Hon. Salisu Majigiri Yace yai tunanin koda yazo malumfashi zai tadda garin mulumfashin yasamu cigaba mai tarin yawa kasan cewar mazabar majalissar tarayya ta Gwamnan katsina na yanzu Hon. Aminu Bello Masari,

Saidai kash yazo ya ganta ba yadda yai tunani ba karshe yace wannan nasara da jam’iyyar PDP take samu a garin mulumfashi wanda cikin Sati guda sun karbi sama da mutum 5000 duk acikin wannan karamar hukuma ta mulumfashi wannan bai rasa nasaba da kyankyawan shugabanci da keda kwai a karamar hukumai da jiha baki daya, Sannan kuma yatabbatar da cewa za su bai wa Hon. Lawal Yusuf duk wata dama da ake ba ýaýan jam’iyyar PDP, kuma za su yi tafiya tare da shi kafaďa da kafaďa don ķara bunķasa jam’iyyar PDP a karamar hukumar Malumfashi da jihar Katsina baki ďaya.

Manyan baķin da suka halarci taron sun hada Matemakin Ciyaman na jiha Hon. Salisu Lawal Uli, Shugaban matasa na jiha Hon. Dahiru Dambo ingawa, Sakataran kudi na jiha Abu lawal kankara, Mai binciken kudi na jiha Alh.Yusuf Abubakar fele, Alhaji Hadi Mai dawa Elder, Hon. Muntari Ibrahim, Tsohon Dan takarar Majalissar Tarayya Kafur/Malumfashi Hon. Murtala Shehu, Alhaji Yakubu Wada, Alhaji Muntari dadai sauron su, An yi taro lafiya kuma an tashi lafiya.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Har yanzu: Gwamna Masari na Alhinin Rasuwars Kwamishinan Kimiyya Rabe Nasir

Gwamna Aminu Bello Masari ya kara bayyana rasuwar Dokta Rabe Nasir a matsayin babban rashi duba da yadda yake da jajircewa tare da sadaukarwa...

Katsina lawyer in court over alleged cheating,forgery, impersonation

A Funtua based Company in Katsina state, NAK International Merchant has dragged a Lawyer, Barrister Mahdi Sa'idu to court over alleged cheating, forgery and...

The YOUTHS ASK YAHAYA BELLO FOR PRESIDENT MOVEMENT (YAYBP) under the Leadership of their Founder/National Coordinator Alhaji Ibrahim Muhammad on Saturday 15th January, 2022...

The movement, which said the gesture is part of its efforts to alleviate the sufferings of the less privileged in the society through its...

Bin Sa’id Tsangaya Model School Ta Yi Bikin Saukar Dalibai.

Daga Auwal Isah. A karon farko, Makarantar hardar Alkur'ani mai tsarki ta " Bin sa'id Tsangaya Model School " da ke a unguwar Tudun 'yan...

Sanata Bola Ahmed Tinubu Ya Kawo Ziyarar Ta’aziyyar Rasuwar Kwamishina Rabe Nasir A Jihar Katsina

Ziyarar Da Jigon Jam'iyyar APC Na Kasa, Tsohan Gwamnan Jihar Legas, Sanata Bola Ahmed Tinubu Ya Kawo A Jihar Katsina, Domin Yin Ta'aziyyar Rasuwar...