SHUGABA BUHARI ZAI HALARCI TARO KAN SAMAR DA KUƊAƊE GA AFIRKA DAZA’AYI A PARIS, ZAI KUMA GANA DA SHUGABA EMMANUEL MACRON KAN TSARO.

Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Bangaren Rediyo da Talabijin.

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Lahadi 16 ga watan Mayu 2021, zai Tashi daga Abuja zuwa Birnin Paris Kasar Faransa, don ziyarar aiki na kwanaki 4 don halartan Babban taro kan yadda za’a sama wa Afirka kudade, taron wanda zaifi maida hankali kan sake dubi game da Tattalin arziki biyo bayan jikkata da yayi sakamakon annobar Cutar Korona, da yadda za’a saukaka musamman Karuwar nauyin bashi ga kasashen.

Babban Taron, wanda Shugaba Emmanuel Macron zai karbi bakwanci, zai ja hankalin manyan masu zuba Jari kan Cibiyoyin samar da kudade na Duniya da wasu cikin Shugabannin Gwamnatocin kasashe, wanda baki dayansu zasu tattauna kan yadda za’a samar da kudade daga waje dama yadda za’a magance bashi dake kan Afirka, sai kuma yadda za’ayi gyare-gyaren fuska kan Bangaren kasuwanci masu zaman kansu.

A yayin Ziyarar, Shugaba Buhari zai gana da Shugaban Ƙasar Faransa don tattauna Karuwar barazanar tsaro a yankin Sahel da Tafkin Chadi da Dangantakar Siyasa, alakan kasuwanci, sauyin yanayi dama kuma hada kai don aiki tare a Bangaren Kiwon lafiya, musamman dubi kan yaduwar Cutar Korona, da kara yin bincike da samar da Rigakafi.

Kafin ya dawo gida Najeriya, Shugaba Buhari zai karbi wasu muhimman masu ruwa da tsaki a Bangaren Mai da Iskar Gas, Injiniyoyi da Sadarwa, da majalisar Turai da wakilai kungiyar Tarayyar Turai kan harkokin kasashen ketare da tsara Tsaro da Membobin kungiyar Ƴan Najeriya mazauna Kasar.

Shugaban Ƙasa zai samu rakiyar Ministan Harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, Ministan kudi da Kasafi da tsare tsare na ƙasa, Zainab Shamsuna Ahmed, sai kuma Ministan Kasuwanci da zuba Jari, Otunba Adeniyi Adebayo, da Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire.

Har ila yau cikin Tawagar akwai: Mai bada Shugaban Ƙasa Shawari kan harkokin Tsaro, Manjo Janaral Babagana Mohammed Monguno Mai Ritaya, da Babban Darakta Hukumar Tattara Bayanan Sirri na Ƙasa (NIA) Ambassado Ahmed Rufa’i Abubakar.

Mal. Garba Shehu:
Babban Mai Tallafawa Shugaban kasa A Kafofin Watsa Labarai da Wayar da kan Jama’a.
15 ga watan Mayu, 2021

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here