Advert
Home Sashen Hausa SHUGABA BUHARI YAYI GARGADI KAN NUNA KYAMAR KABILANCI KO ADDINI

SHUGABA BUHARI YAYI GARGADI KAN NUNA KYAMAR KABILANCI KO ADDINI

SHUGABA BUHARI YAYI GARGADI KAN NUNA KYAMAR KABILANCI KO ADDINI

Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Bangaren Rediyo da Talabijin.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ranar Alhamis a Abuja yayi gargadin cewa chakala yin kyamar kabilanci ko addini bazai samar wa kasar Cigaba ba, ya kara da cewa Gwamnatin sa zata cigaba da samar da yanayi mai kyau ga ‘yancin gudanar da Addini kamar yadda dokar kasa ta bada tabbacin haka.

Da yake Magana a lokacin da Shugaban nin Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Islama NSCIA karkashin Jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar, suka kawo masa Ziyara.

Shugaba Buhari yace

“Gwamnatin Tarayya zata cigaba da Dabbaka ‘yancin yin Addini kamar yadda dokar kasa ta samar da hakkin hakan. Ya zamo dole na Godewa Al’umman Musulmi kan dabbaka Tattaunawa tsakanin Addinai ma banbanta a kasa. Hujjace garemu cewa idan muna son kasar mu ta dore, dole mu cigaba da aiki tare dukda banbancin Kabila, Addinai da Siyasa Sakamakon kasar tamu ce gaba daya.

“Sa’annan kuma Gwamnatin Tarayya karkashin Shugaban ci na bata kuma bazata taba bari kyamatar Addini ko bangaranci yayi tasiri ga matakai da tsare-tsaren ta ba. Ya zamo shawari na na hakika nayi adalci ga dukkan bangarorin Al’umma.”

Shugaba Buhari ya bada tabbaci ga wakilan cewa Gwamnati tana yin duk abinda ya dace cikin ikon da take dashi domin rage yawan halin rashin tsaro da yanzu ake fama dashi, ya kuma yi kiraga Al’umman karkara da su taimaki Jami’an tsaro a yayin gudanar da aikin su:

“Gwamantin Tarayya tana aiki ka’in da Na’in domin yaki da rashin tsaro da sauran Matsaloli dake addaban kasa. Rashin tsaro wace matsala ce dake daukan lokaci to amma bazamuyi kasa a gwiwa gurin kokarin da muke. Ba kawai Samar wa Soji makamai da suka dace ba, a a muna kuma karfafa musu kwarin gwiwa domin sauke nauyi da Dokar kasa ta daura musu ba tare da wani tsaiko ba. Muna kuma karfafa gwiwar yankuna da rashin tsaro suka tabaibaye kan su kara sanya ido da tattara bayanan Sirri da Mikawa ga Jami’an tsaro.

“Na amince cewa harkan tsaro shine hakkin na farko kan Gwamnati to amma Gwamnatin kadai bazata iya ba. Harkan na bukatar masu ruwa da tsaki, kamar ku kan ku.

A saboda haka, Ina kwadaita muku ku bada gudumowa ga Jami’an tsaro ta hanyar Samar musu da bayanan da zai kara kawar da rashin tsaro a tsakanin Al’umma.”

Shugaban ya kumayi magana kan kokarin Gwamnatin sa kan abinda yashafi kokarin inganta rayuwar ‘yan kasa marasa galihu:

“Muna Sauya yanayin tsarin arzikin kasar mu da bada fifiko ga samar da abubuwa da suka dace domin rage talauci da kara Dacewa gurin yaki da Cin hanci da Rashawa, ba tare da la’akari da matsayin wadan da abin ya shafa ba.

“Shirye Shiryen Gwamnatin mu kamar su Npower, Bada kudi ga Marasa Galihu, Shirin Gwamnati na tallafawa ‘yan kasuwa, da Shirin ciyar da yara ‘yan makaranta wasu kadan ne cikin shirye shiryen da muka kawo domin taimaka wa ‘yan Najeriya gurin biyan bukatun kansu.

“Shirin Samar da Tallafi na kasa shi kadai ya anfanar da ‘Yan Najeriya Mutum Miliyan Hudu ta hanyan samun horo kan abin dogaro da tallafin kudi.”

Shugaba Buhari yayi kira ga Shugaban nin da su cigaba “Da yin magana ga Al’umman mu da Isar da sakon ta hanyoyi da suka da che” da kuma bada cikakken goyon baya ga Shirin ciyar da yara ‘Yan makaran ta Wanda ya kaddamar ranar Talata.

Yace akwai “Tsari bama kawai don magance yawan yara da basa zuwa Makaranta ba, hakan kuma zai kara karfafa Ilmi ga ‘ya’ya Mata yayin da zai kuma samar wa Matasa abinda ya dace gurin zabawa kawunan su hanyar sauya rayuwar su a yayin da suke tun kara masu yada sakonnin tsana dama kuma magance matsalar kiwon lafiyar Al’umma da yanzu Duniya ke Fuskanta.

Shugaban yayi imfani da wannan dama don rokon ‘Yan Najeriya da su mara baya ga Gwamnati a kokarin ta na yaki da Cutar Korona:

“A dai dai Sa’ilin da Gwamnati ke cigaba da aiki don ganin ta magance wannan rikici, yana kuma da muhimmanci cewa kun sanya muryoyin ku gurin mara baya wa wadan nan abubuwa da suka wajabta na bin tsare-tsare da zasu iya taka rawa gurin dakile yaduwar kwayar Cutar, wanke hannayen mu, yin amfani da Takunkumin Fuska, da tabbatar da bada tazara da sauran matakai da suke nan, hakan ya shida shine mataki na farko na kariya a yaki da kwayar cutar.

“Kari game da haka da sauran muhimmin abu, shine yayin da Rigakafi wanda muna aiki ba dare ba rana domin sayowa da kawo shi kasa, Ina rokon ku kubi sahun wayar da kan Mutane kan cewa wannan allura anyi shine domin bada kariya ga kowa da kowa da tseratas wa.”

Tun da farko cikin Jawabin sa Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ya yabawa Shugaban kasa kan Nasara daya Cimma a yankin Arewa maso gabas, Yayi kira ga Gwamnati data Magance Barayin Daji dake addaban yankin Jihohin Arewa maso Yamma Zamfara, Sokoto, da wasu sassan Shiyar Arewa ta Tsakiya.

Yayin kuma daya bayyana kwarin gwiwar cewa Jami’an tsaro idan aka samu hada karfi da karfe a cikin su za’a shawo kan Matsaloli da ake ciki yanzu, Sarkin yakuma yi roko na samun goyon bayan dukkanin Gwamnoni da Gwamnatin Tarayya ba tare da la’akari da Banbancin siyasa ba, ya kumayi kira ga dukkanin ‘yan Najeriya dasu goya baya ga Sabbin Shugabannin tsaro.

Shugaban nin na Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci NSCIA, sun kuma roki ‘yan Najeriya, Musamman Shugabannin Addinai da su guji yin kalaman Takala da zai iya kawo sabani da kara lalata yayin rashin tsaro da ake ciki a kasa. Yayi bukaci a ja hankalin Shugaban nin Addinai da suke kalaman dazai hambarar da Gwamnati.

Haka nan kuma Mai Alfarma Sarkin Musulmai yayi Na’am da “Gangamin yaki da kalaman Nuna Tsana” da Ministan Yada Labaru da Al’adun Gargajiya ke jagoranta. Yace ‘Kalaman Nuna Kyaman Juna’ yana kara Munana Rashin Tsaro a kasa saboda haka “Dole a dau mataki akai”

Mal. Garba Shehu:
Babban Mai Tallafawa Shugaban kasa A Kafofin Watsa Labarai da Wayar da kan Jama’a.
28 ga watan Janeru, 2021

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Babu wanda zai bar jami’a saboda bai biya kuɗin makaranta ba -Farfesa Muhamad Sani Tanko

Babu wanda zai bar jami'a saboda bai biya kuɗin makaranta ba – Farfesa Muhammad Sani Tanko, Shugaban Jami’ar Jihar Kaduna ya kawar da tsoron da iyayen...

Police Arrest 60-Year-Old Man Conveying Rifles In Car Bonnet

A 60-year-old man, Umar Muhammed, was arrested while conveying firearms across the country. The suspect uses his vehicle to transport rifles concealed in the bonnet...

TABBAS ZA AYI ZABEN SHUGABANNIN APC …inji bagudu

TABBAS ZA AYI ZABEN SHUGABANNIN APC ...inji bagudu @katsina city news Gwamnan jahar kebbi bagudu ya tabbatar ma da Manema labarai a Abuja cewa tabbas za...
%d bloggers like this: