Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Bangaren Rediyo da Talabijin.

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya kaɗu sosai da jin Rasuwar Mutane 29 a sanadin Hatsarin jirgin Kwale-Kwale a Kogin Shagari, garin Gidan Magana karkashin Yankin Ƙaramar Hukumar Shagari jihar Sokoto.

Shugaban ya mika sakon Alhinin sa ga Iyalan wadan da suka rasa Ƴan-uwan su a yayin Hatsari mai tada hankali, Musamman Sarkin Kauyen Gidan Magana, Malam Muhammadu Auwal, wanda ya rasa Yaran sa Biyar a yayin Hatsarin.

Shugaba Buhari ya Umarci Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa Nigeria Inland Waterways Authority (NIWA) kan su kara kokari da suke don tabbatar da kiyaye masu tafiye tafiye ta ruwa a Najeriya.

Shugaban Ƙasar, wanda ya kuma jajanta wa Gwamnati da Al’umman jihar Sokoto, yayi Addu’an Allah yaji Kan wadan da suka rasa rayuwar su, ya bada hak’urin Juriya ga Iyalan su.

Mal. Garba Shehu:
Babban Mai Tallafawa Shugaban kasa A Kafofin Watsa Labarai da Wayar da kan Jama’a.
14 ga watan Afrilu, 2022

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here