Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Bangaren Rediyo da Talabijin.

Jam’huriyar musulunci na Pakistan zata ci gaba da zama mai aminci da kuma abokiya cikin tallafawa Najeriya, musamman cikin horon jami’an tsaron sojoji, inji Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Shugaban kasa yayi wannan magana ne a ranan juma’a a fadan shugaban kasa a Abuja, a lokacin da ya karbi Janar Nadeem Raza, shugaban rundunar hadin gwiwa na shugaban kwamitin jam’huriyan musulunci.

Shugaban kasa yace: “mun yaba muna akan godiya kwarai kan taimakon ku cikin bada horo ma jami’an tsaron mu na sojoji, da kuma wasu daga cikin abokaina sun samu horo ne a kasan ku, kuma da ku ci gaba da zama abokai cikin taimaka mana. kuma mu muna godiya.”

Janar Raza yace Najeriya ta kasance mai muhimmanci sosai cikin kasashe a nahiyar Afirka, kuma mu muna daraja wannan hadin gwiwa. mu mun yi koyi kuma mun amfana sosai daga kowani bangare.”

Femi Adesina:
Mashawar ci Na Musamman ga Shugaban Kasa a Fannin Yada Labaru da Wayar da kan Jama’a.
2, ga watan Yuli na Shekarar 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here