Rahotanni sun bayyana cewa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya tsallake faruwar haɗarin jirgin sama, yayin da jirgin sa ya samu matsala.

Shugaba Buhari ya je ƙasar Saudiyya ziyarar aiki inda daga nan kuma ya yi aikin Umrah.

Jirgin na shugaban kasa ya samu matsala inda daga bisani aka tafi da shi ƙasar Jamus dan gyarawa.

Majiyar mu ta Sahara Reporters ta bayyana cewa ana kashewa jirgin naira miliyan 2.4 duk dare a wajan gyaran da aka kaishi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here