YANZU-YANZU | Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari da Ministocin sa da shugabannin tsaron Najeriya sun shiga taron majalisar tsaro na kasa.

Wannan shine dai zama na farko da shugaba Buhari zai yi da sabbin shugabannin tsaron Najeriya tun bayan nada su.

Daga cikin mahalarta taron akwai mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo, Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Gida Mustapha, shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya, Farfesa Ibrahim Gambari, da mai bawa shugaban kasa shawara akan tsaro Janar Babagana Monguno (mai Ritaya).

Sauran mahalarta taron sun hadar da ministan tsaron kasa, ministan harkokin cikin gida, ministan harkokin ‘yan sanda da ministan harkokin kasashen waje, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi (mai Ritaya), Ogbeni Rauf Aregbesola, Muhammad Dingyadi and Mr Geoffrey Onyema.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here