SHUGABA BUHARI YA GANA DA SHUGABAN FARANSA MACRON, YA SAMU TABBACI BASHI GOYON BAYA.

Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Bangaren Rediyo da Talabijin.

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari tare da Takwaran sa, Emmanuel Macron sun tsaya kan Alkawarin cewa kasashen biyu zasu yi aiki tare don yakar rashin tsaro dake addabar yankin Tafkin Chadi da daukacin yankin Sahel.

A lokacin da yake magana a yayin taron hadin kai, wanda ya karbi bakwancin Shugaban Najeriya a gefen Babban taro bunƙasa Tattalin arzikin Afirka ranar Talata a Birnin Paris, Shugaba Macron yayi Alkawarin tsayawa don bada goyon baya ga Najeriya da Al’umman ta a daidai lokacin da suke fuskantar kalubale na rashin tsaro dake fuskantar Ƙasar.

Shugaba Macron yace, Gwamnatin Faransa zata kasance tare da Najeriya dakuma aniyar mara mata baya da duk abinda ya dace don taimakawa Kasar Gurin shawo barazanar Rashin Tsaro.

Shugaban ya kuma yi Alkawarin goyon bayan Najeriya don tunkarar kalubale dake tattare da Rigakafin Cutar Korona.

Shugaba Buhari, a yayin taron, ya zayyano kalubale da duk ke fuskanta Kasar dama kuma makwabtan ta yakuma yi magana akan matakai da yake dauka don magance yanayin, wanda yace sun kunshi sake Naɗa Sabbin Hafsoshin Tsaron Ƙasa.

Shugaban Ƙasar ya nuna bukatar Najeriya nayin aiki tare da ƙasar Faransa dama dukkanin kasashen dake da bukatar aiki tare don ƙauda kalubalen rashin tsaro, ya gode wa Shugaba Macron na amince da kara ƙaimi kan aiki tare da Kasar keyi da Najeriya.

Mal. Garba Shehu:
Babban Mai Tallafawa Shugaban kasa A Kafofin Watsa Labarai da Wayar da kan Jama’a.
18 ga watan Mayu, 2021

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here