Shugaba Buhari Ya Baiwa Kwamitin Rage Talauci Umurnin Gaggauta Ceto Mutane Milyan Dari Daga Talauci A Najeriya

A ranar Talata, 22 ga watan Yuni, 2021, Shugaba Muhammadu Buhari, ya kaddamar da kwamitin da aka ba alhakin rage talauci da bunkasa tattalin Arzikin Nijeriya.

Ana so wannan kwamiti da yake karkashin mataimakin shugaban kasa, Farfesa, Yemi Osinbajo, da su gaggauta ceto mutum miliyan 100 daga halin talauci a fadin kasar.

Mai girma Muhammadu Buhari ya yi alkawari gwamnatinsa ta tsara dabarun da za ta bi domin ceto mutanen da talauci ya yi daurin goro nan da shekaru goma.

Mai magana da yawun bakin shugaban kasa Femi Adesina, ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar.

Da yake magana a bikin rantsar da wannan kwamiti, jaridar Punch ta ce shugaban kasar ya bayyana dabarar da kwamitin NPRGS za ta bi wajen yin wannan aiki.

Muhammadu Buhari ya ke cewa an soma aikin ne tun Junairun 2021 lokacin da ya bukaci majalisar masu ba shi shawara kan tattalin arziki su yi maganin fatara.

Premium Times ta rahoto shugaban Nijeriyar ya na cewa za ayi maganin duk kura-kuren da aka yi a baya, a fito da tsarin da zai azurta miliyoyin mutanen da ke kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here