Advert
Home Sashen Hausa SHUGABA BUHARI YA AMINCE DA YIN GARAMBAWUL GA MAJALISAR MINISTOCI

SHUGABA BUHARI YA AMINCE DA YIN GARAMBAWUL GA MAJALISAR MINISTOCI

Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Bangaren Rediyo da Talabijin.

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da yin garambawul a majalisar ministocin da aka kafa ranar 12 ga Ogustan, 2019.

Cikin sanarwa ga membobin Majalisar a yayin zaman majalisa zartaswa ranar Laraba 1 ga watan Satumba, Shugaba Buhari ya sanar cewa Ministan aikin Gona da raya Ƙarƙara Mohammed Sabo Nanono, da Ministan Lantarki, Injiniya Sale Mamman an sallame su a bakin aiki.

A gefe guda kuma, Dakta Mohammed Mahmood Abubakar, Ministan Muhalli, an sauya mishi Ma’aikata zai fara aiki a Matsayin Ministan Noma da Cigaban ƙarkara, yayin kuma da Injiniya Abubakar D Aliyu, karamin Ministan Aiyuka da Gidaje yanzu ya zamo sabon Ministan Lantarki.

Shugaban yace, sauyin bisa “Al’adar samun daidaita aiwatar da aiyuka da shirye shirye don dogara dama sake dubi kan Muhimmanci” ta hanyar bada rahoton bangarori a yayin taro majalisar zartaswa.

Ya kara da cewa, wadan nan Muhimman Mayakan yin nazari ya taimaka Gurin gano da karfafa gurare da keda koma baya, kusanto da rata, gina aiki tare da hadin gwiwa cikin aikin gwamnati, tafiyar da tattalin arziki da inganta Samar da abubuwan Gwamnati masu kyau ga Ƴan-Nijeriya.”

Femi Adesina:
Mashawar ci Na Musamman ga Shugaban Kasa a Fannin Yada Labaru da Wayar da kan Jama’a.
1st ga watan Satumba, 2021

Ga Cikakken bayanin a nan ƙasa:

A ranar Laraba 21 ga watan Ogusta, 2019, an rantsar da Majalisar zartaswa ta yanzu bayan doguwar tuntuba don samar da Sabbin Membobi da maido da wasu don hanzarta kammala aiyukan da aka fara, kalubale da maida hankali ga wasu darusa da aka gajesu daga zango mulki na na farko don karfafa Muhimman gurare 9 da muka basu fifiko, a zango na biyu.

2. Shekaru biyu da Ƴan watanni a zango na biyu, Al’adar al’adar samun daidaita aiwatar da aiyukan mu, da shirye shirye don dogara dama sake dubi kan Muhimmanci sun samu tushe ta hanyar bada rahoto yayin zaman majalisar zartaswa.

3.Wadan nan Muhimman mataki na sake dubi ya taimaka Gurin gano da karfafa gurare masu koma baya, da cike rata, da gina aiki tare da hadin gwiwa a aikin gwamnati, tafiyar da tattalin arziki da karfafa aikin gwamnati mai kyau ga Ƴan-Nijeriya.

4. Dole na godewa wa wadan nan Majalisa kan nuna jajircewa wanda ya taimaka wa Gwamnati Gurin daƙile tsaiko da tsaron duniya da tafiyar da hidimar Gwamnatoci sakamakon bullar Cutar Korona, Jim kadan bayan kaddamar da majalisar.

Al’adar taron Majalisar zartaswa a mako mako bai samu yadda yake so ba, saboda yana yi da Cutar dazo dashi.

5. Kamar yadda duk muka sani, sauyi Shine kawai ya zamo da’iman a duk wani niyya Dan’adam, wannan Gwamnati tana tunkarar Muhimman gurare a wannan zango na biyu, Na gano muhimmanci Gurin sake karfafa gwiwa ga wannan Majalisa ta hanyar sake Karfafa aiyuka don samar da nasarori dazasu kafa tarihi.

6. Bisa tsari, na amince da sauye sauyen kadan daga membobin Majalisa, hakan ya samar da turban Cigaba.

Kamar yadda ke biye:

Ministocin da aka sallama sune:

1. Mohammed Sabo Nanono, Ministan Noma da Cigaban Ƙarƙara.

2. Injiniya Sale Mamman, Ministan Lantarki.

Sake guraben aiki.

1. Dakta Mohammed Mahmood Abubakar, Ministan Muhalli, zai kama aiki a Matsayin Ministan Noma da Cigaban Ƙarƙara.

2. Injiniya. Abubakar D. Aliyu Ƙaramin Ministan aiyuka da Gidaje, ya kama aiki a Matsayin Ministan Lantarki.

7. A lokacin mafi Dacewa, za’a fidda wadan da zasu cike guraben da suka ma’aikatun da suka bari kamar yadda dokar kasa ta shimfida.

8. Ni da kaina na zauna da ministocin da muka sallama don yi musu Godiya kan Gudumowar tattaunawa a Majalisar zartaswa da gagarumin aiki da sukayi wa ƙasa. Yau, ya kasance rana ta karshe garesu dazasu halarci taron Majalisar zartaswa, Ina musu fatan Alkhairi a niyyar su na gaba.

9. Daga Ƙarshe, Ina fata kara Jaddada cewa, irin wannan mataki za a cigaba da yin sa.

10. Ina gode muku baki daya, Allah ya albarkaci Gwamnatin Tarayya Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Shugaba Buhari ya nemi kasashen duniya su yafewa Najeriya bashin da suke binta

A yayin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya a ranar Juma'a. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi manyan kasashen duniya...

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina Saifullahi Kuraye‎ September 24, 2021 2 min read Bangaren aikin jarida na...

Hukumar Hana Fasa ƙwabri ta ƙasa wato Custom ta ƙwato Babura Ɗari Biyu da Biyu a Jihar Katsina…

Shugaban Hukumar Ƙwastam na Jihar Katsina Mr. Chedi ne ya bayyana hakan ne a Yau Juma'a cewa tsakanin watan Agusta zuwa Satumba Hukumar ta...

Dan Najeriya ya fiye tsogwami: da ₦500 kacal sai aci a ƙoshi……Inji farfesa Segun Ajibola

Da Naira Dari Biyar ( 500 ) kacal Zaka Iyaci Ka Koshi a Najeriya, Cewar Wani Farfesa, Masanin Tattalin arziki... Tsohon shugaban kwalejin ma'aikatan bankin...

Rail project will not displace host communities-FG

Radio Nigeria The Federal Ministry of Transport and that of Environment have given assurance to residents along the proposed stretch of land demarcated for the...
%d bloggers like this: