Ba lallai ne Buhari ya miƙa mulki ga mataimakinsa ba – Fadar Shugaban Ƙasa

Buhari

Ba lallai ne sai Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya miƙa mulki ga mataimakinsa ba sakamakon tafiya Landan da ya yi, a cewar fadar shugaban ƙasa.

Mai taimaka wa Buhari na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Garba Shehu, shi ne ya bayyana hakan a yammacin Talata yayin da ya bayyana ta cikin shirin Politics Today a kafar talabijin ta Channels.

Ya ƙara da cewa mai gidan nasa bai karya wata doka ba don bai miƙa mulki ga Farfesa Yemi Osinbajo ba saboda ya fita daga ƙasar ne na ‘yan kwanaki kawai.

“Zai ci gaba da aiki duk daga inda yake,” in ji Garba Shehu.

“Abin da doka ta tanada shi ne, idan shugaban ƙasa zai kai kwana 21 ko fiye a waje, to sai ya miƙa mulki. A irin wannan yanayi na yanzu bai zama dole ba.”

Buhari ya yi balaguro zuwa Birtaniya a lokuta da yawa tun bayan hawansa mulki, amma wannan ne karon farko da ya je ƙasar tun bayan ɓullar annobar korona.

Fadar shugaban ta ce ana sa ran zai koma Najeriya a makon farko na watan Afrilu mai kamawa.

A 2017, ya shafe kwana 103 yana jinya a Landan, inda Osinbajo ya zama muƙaddashin shugaban ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here