Daga Comr Abba Sani Pantami

Kungiyar Manoman Shinkafa ta Nijeriya (RIFAN), ta ce noman shinkafa a kasar ya karu daga tan miliyan biyu a 2015 zuwa tan miliyan tara a 2021, Daily Nigerian ta ruwaito.

Da yake bayyana hakan a Kaduna a ranar Alhamis, Shugaban RIFAN, Aminu Goronyo, ya ce duba da yawan kayan da ake sarrafawa a yanzu, Najeriya ta shirya zama kasar da zata ke fitar da shinkafa zuwa kasashen waje.

A cewarsa: “Kafin zuwan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2015, mun saba samar da kimanin shinkafa tan miliyan biyu a shekara.

“A yau, za mu iya alfahari da tan miliyan tara a shekara; akwai bambanci sosai kuma yanzu za mu iya cewa balo-balo Najeriya ta wadatu da shinkafa.”

Game da tsadar abinci: Ba fa zai yiwu mu yi kasa da farashin buhun shinkafa ba inji ‘Yan kasuwa.

Sai dai har yanzu talakawa a Najeriya na kokawa kan tsadar da abinci ya yi, musamman shinkafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here