Advert
Home Sashen Hausa SHIN KAIMA/KEMA/KUMA KUN YARDA DA CEWAR MUNTARI LAWAL ZAI IYA ƁATA RAWAR...

SHIN KAIMA/KEMA/KUMA KUN YARDA DA CEWAR MUNTARI LAWAL ZAI IYA ƁATA RAWAR SHI DA TSALLE?

A ranar asabar 31-07-2021 jam’iyar APC ta gudanar da zaben shuwagabannin jam’iyar APC a matakin gunduma ko unguwanni guda dari ukku da sittin da ɗaya a fadin jahar Katsina (361 ward Congress). Kuma duk mutumin dake bin siyasar jahar Katsina ko kana Apc ko ba ka Apc babu mai inkarin cewar zaben bai da sahihanci.

Shin me ya kawo sahihancin zaben?

Kowa ya aminta da kwamitin da ya gudanar da zaben a jahar Katsina cewar 90% ya gudanar da zaben bisa adalci sai dai ajizanci na dan Adam. Kuma da yan takarar kujerun, da ‘yan takarar gwamna da na sanatoci, da na Reps, da majalisar jaha kowa ya gamsu da sahihancin zaɓen.

Haka zalika ranar 04-09-2021 an gudanar da zaben shuwagabannin jam’iyar APC a matakin ƙananan hukumomi 34 na jahar Katsina wanda shi ma zaben kowa ya aminta da cewar an yi adalci sai dai dan abinda ba a rasa ba wanda ajizanci ne na dan Adam kowa na da irin nasa, amman dai mutane kusan 95% kowa ya gamsu. Ko a haka aka tsaya a iya cewa Shugaban kwamitin ya ciri tuta, saboda jahar Katsina na cikin jahohi ukku a Najeriya wacce a ke kwatance da ita kan kyawawan zabukan da aka gudanar a jahar kasancewar ta jahar Shugaban ƙasa.

Yanzu haka jam’iyar APC ta ƙasa ta saka ranar asabar 02-10-2021 a matsayin ranar da za a gudanar da zabukan shugabancin jam’iyar a matakin jahohi 36 duk da Abuja da bakwai. Kawo yanzu a iya cewa kallo ya koma sama kan cewar shin wannan zaben da zai gudana zai yi inganci kamar wadancan zabukan da suka gabata ko kuwa a’a kwamitin zai bata rawar shi ne da tsalle?

Yanzu jama’ar jahar Katsina sun zuba idanu su gani cewar shin kwamitin zai yi abinda kaso mafi rinjaye na al’ummar jahar Katsina za su gamsu ko kuwa a’a?

Babu mai amsar wannan tambayar har sai abinda ranar asabar ɗin 02-10-2021 tayi tukuna. Yanzu haka akwai kingiyoyin fararen hula da na sa kai da zasu saka idanu kan zaben wasu daga cikin gida wasu kuma daga wajen jahar ta Katsina kasancewar jahar Katsina jaha ce ta Shugaban ƙasa.

Jamilu Hassan Dutsin-Ma
23-09-2021

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

ADMISSION FORM IS AVAILABLE @ SILICON HEIGHT INTERNATIONAL COLLEGE KATSINA.

SILICON HEIGHT INTERNATIONAL, SCHOOL WISHES TO INFORM THE GENERAL PUBLIC THAT,THE SALE OF FORMS INTO NURSERY, PRIMARY AND SECONDARY IS STILL ONGOING. THE SCHOOL...

Gwamna Aminu Bello Masari ya buɗe taron shuwagabannin Majalisun jihohin Najeriya a Katsina…

Mai girma Gwamnan Jihar Katsina ya bude taron shugabannin majalisun Dokokin Jihohin Najeriya (36) a kwata na uku, da Jihar ta dauki bakunci. Taron da...

Jihar Katsina ta amshi bakuncin Kakakin majalisun Dokokin Jihohin kasar (36).

A cikin shirye, shiryen gudanar da Babban taron Kungiyar wanda ta sabayi lokaci bayan lokaci, domin tattauna al'amurran da suka shafi kasa. Taken taron na...
%d bloggers like this: