Hassan Male @Katsina City News

An kashe mutum 636 a watan Oktoba kaɗai a sassan Najeriya.

Wannan na kunshe ne a wani rahoto da Kamfanin Beacon Consulting ya fitar. Kamfanin dai ya saba duk wata yakan fitar da rahoto kan binciken da ya yi game da matsalar tsaro a Najeriya tare da bayar da shawarwari ga mahukunta.

Rahoton kamfanin ya ta’allaqa ne kan jihohi 33 na Najeriya a ƙananan hukumomi 105.

Alƙalumman sun nuna an samu raguwar yawan adadin waɗanda aka kashe a Najeriya a watan Oktoba idan aka kwatanta da rahoton watan Satumba inda alƙalumman suka ce an kashe mutum 663.

Sai dai rahoton ya ce wata na huɗu kenan a jere da aka samu sama da mutum 600 da aka kashe a Najeriya tun a Yuni, watan da aka fi kashe mutane a Najeriya a 2021 inda aka kashe mutum 1031.

A cewar rahoton alƙaluman sun haɗa da yawan mutanen da aka kashe sakamakon rikicin Boko Haram, da kuma na ƴan fashin daji a arewa maso yammacin Najeriya da ma waɗanda jami’an tsaro suka kashe a bakin aiki, da kuma su kansu jami’an tsaro da suka rasa rayukansu a fagen daga.

Da kuma ƙaruwar laifuka a yankin kudu maso yammacin Najeriya da ya haɗa da fasa gidan yari da aka yi a jihar Oyo da tasirin yunƙurin Najeriya na hukunta shugaban ƴan a waren Biafra Nnamdi Kanu wanda ke ƙara ingiza mambobin IPOB da ƙaruwar rikici a kudu maso kudu da kudu maso gabas.

Rahoton ya bayyana cewa yanayin ya sauya daga arewaci zuwa kudanci, inda kudu maso yammaci da kudu maso gabas aka samu ƙaruwar kashi 22 idan aka kwatanta da kashi 19 a arewa maso yammaci da arewa ta tsakiya. Kudu maso kudu da arewa maso gabas an samu ƙaruwar kashi tara.

Sai dai duk da sauyin, adadin waɗanda aka kashe bai sauya ba, inda a arewa maso yammaci aka kashe mutum 258, a arewa maso gabas mutum 158.

A yankin arewa ta tsakiya mutum 109 aka kashe, a kudu maso gabas mutum 65, yayin da a kudu maso yammaci aka kashe mutum 30, mutum 16 a kudu maso kudu.

Amma rahoton ya ce an samu raguwar matsalolin tsaro a arewa maso yammaci da kashi 47 tsakanin Satumba zuwa Oktoba, haka ma a arewa ta tsakiya da kashi 39.

Rahoton ya kuma ce an samu raguwar hare-haren ƴan bindiga masu fashin daji a jihohin Kaduna da Katsina da Sokoto da Zamfara saboda matakan da hukumomi suka ɗauka na tsaro da suka haɗa da katse hanyoyin sadarwa da hana cin kasuwannin maso da kuma ayyukan hakar ma’adinai.

Sai dai kuma a cewar rahoton an fi samun ƙaruwar hare-haren a jihar Sokoto a watan Satumba duk da matakan da aka ɗauka.

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, ko a yan’ kwanakin nan, akalla mutane 12 be aka kashe a yankin Batsari ta jahar Katsina. A jahar Zamfara ma lamurra na Kara tsananta inda a yan’ kwanakin nan, barayin dajin suka kashe jami’an yan’sanda mutum 7 banda sauran hare hare da ke faruwa a yankunan karkara.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here