Home Sashen Hausa Shi ma Joe Biden zai kai ƙara kotu

Shi ma Joe Biden zai kai ƙara kotu

Shi ma Joe Biden zai kai ƙara kotu

Joe Biden

Kwamitin karbar mulki na zaɓabben shugaban Amurka Joe Biden ya ce yana tunanin shigar da kara gaban kotu kan jinkirin da wata ma’aikatar gwamnati ke yi na tabbatar da nasararsa a zaɓen shugaban kasa.

Ana dai bukatar samun amincewar hukumar General Services Administration (GSA), wadda ke tallafa wa ma’aikatun gwamnatin kasar ta Amurka.

Sai hukumar ta amince sannan tawagar Biden za ta samu damar samun miliyoyin dalolin da take bukata na shirye-shiryen karbar mulki.

Sai dai mai magana da yawun hukumar ta GSA, Emily Murphy, ta ce har yanzu shugaban hukumar, wanda Donald Trump ne ya naɗa, bai gama tantance wanda ya lashe zaɓen shugabancin kasar ba, duk kuwa da cewa kafofin yaɗa labarai a kasar sun bayyana Joe Biden a matsayin wanda ya yi nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu – DSS

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu - DSS Rundunar 'yan sandan farin kaya ta DSS ta tabbatar da kama Salihu Tanko Yakasai, tsohon mai taimaka wa...

Ansako ɗaliban makarantar Kagara da aka sace

GSC Kagara: An sako mutum 41 da aka sace a makarantar Kagara ta Jihar Neja An sako ɗaliban makarantar Kagara da malamansu da ma'aikata guda...

PRESS RELEASE ; GANDUJE SACKS MEDIA AIDE

PRESS RELEASE GANDUJE SACKS MEDIA AIDE Governor Abdullahi Umar Ganduje of Kano state has relieved his Special Adviser on Media, Salihu Tanko Yakasai of his appointment...

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 26/02/2021

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 26/02/2021 7 DAYS ACHIEVEMENTS OF CP SAMA'ILA SHU'AIBU DIKKO, fsi IN KANO STATE ... As 9 Kidnapping Suspects, 8 Armed Robbery...

Bamu da Adalci, Dole ne mu cire batun Siyasa idan ba Haka ba Muna gidajenmu zamu Hallaka ~Inji Atiku Abubakar..

Bamu da Adalci, Dole ne mu cire batun Siyasa idan ba Haka ba Muna gidajenmu zamu Hallaka ~Inji Atiku Abubakar.. Tsohon mataimakin Shugaban Kasa Atiku...
%d bloggers like this: