Advert
Home Sashen Hausa SHEKARU ISHIRIN DA BIYAR (25) NA HAKIMCIN SARKIN RAFIN KATSINA A MAIRUWA

SHEKARU ISHIRIN DA BIYAR (25) NA HAKIMCIN SARKIN RAFIN KATSINA A MAIRUWA

A bayyane yake cewar Maigirma Sarkin Rafin Katsina Hakimin Mairuwa Alhaji Sani Idris Sambo ya cika Shekaru 25 a bisa kujerar hakimcin garin Mairuwa. An kirkiro sabuwar Jihar Katsina daga tsohuwar Jihar Kaduna a September 1987 sai dai sabuwar Jihar ta taho da tsoffin kananan hukumomi 7, wanda hakan ya sanya a shekara ta gaba a ranar 15 May 1989 aka kara sabbin kananan hukumomi ciki kuwa har da Faskari LG.

Sabuwar Karamar Hukumar Faskari da aka yanke daga Funtua dama can suna da Hakimi da dadewa (Sarkin Yamman Katsina)kuma suna cin gashin kansu a sarauta. Ita kuma Mairuwa dama can kasar Maska ce , watau mai Headquarters a Funtua tare da Sarkin Maskan Katsina a matsayin Hakimi. Don haka sai Gwamnati da Masarautar Katsina taga bukatar sake kirkirar sabbin gundumomi domin samun daidaito akan zamantakewa.

A dalilin hakanne, aka kirkiro sabuwar Gundumar Mairuwa a cikin 1989 tare da yi mata sabon Hakimi mai lakanin sarautar Magajin Rafin Katsina . Sai dai ba a nada sabon Hakimi ba har sai a January 1991 , yayin da aka kawo Barayan Katsina Alhaji Musa Kafarda yayi Wakilci a sabuwar Gundumar Mairuwa.

Alhaji Usman (Sabo) Idris Sambo dan Sarkin Maska Idiris Sambo (1968-1995) shine Hakimi na farko da aka nada a matsayin Magajin Rafin Katsina Hakimin Mairuwa. Sai dai Allah yayi mashi rasuwa a watan February 1996 sanadiyar kisan gilla da makiyaya sukayi mashi yayin da yake kokarin kare jama’ar shi.

A sanadiyar hakanne aka nada dan uwanshi Alhaji Sani Idris Sambo ya zama sabon Magajin Rafin Katsina Hakimin Mairuwa a ranar 24 May 1996. Bayan wasu shekaru an daga darajar Maigirma Magajin Rafi zuwa Sarkin Rafin Katsina a shekarar 2010 kuma ya cigaba da hakimcin garin na Mairuwa. Kuma shine a yanzu muke tayawa murnar cika Shekaru 25 a wannan mulki.

Maigirma Sarkin Rafin Katsina a shekaru 25 da ya shafe yana mulkin wannan yanki mai albarka, ya kasance mai adalci da kaunar jama’ar shi tare da yunkurin ganin kare mutumcin su a kowane lokaci. Hakan ya sanya ya zama abin so da kauna matuka ga mutanen Gundumar Mairuwa kwata.

Tsawon zamanin Sarkin Rafi , Gundumar Mairuwa ta samu cigaba ainun, ta fannonin ilimi, tattalin arziki, kiwon lafiya, aikin gona da sauran fannoni da dama. Abun farinciki ne mu tuna cewar a lokacin shi ne Mairuwa ta samu manyan makarantun Secondary na Zamani har guda biyu. Haka kuma saboda tsayuwar shi da jajircewa aka kara inganta ayyukan Matsakaiciyar Asibi ta Mairuwa (Comprehensive Health Center ) inda ta zama cibiya ta taimakon marasa lafiya daga garin Mairuwa da garuruwan makwabta. Bisa irin jawo hankali da karfafa gwiwar jama’a bisa ga neman ilimi na Sarkin Rafi, Mairuwa ta samu manyan dalibai da suka zama kwararru a dukkan fannonin ilimi.

Zan iya tunawa lokacin ina Shugaban Kungiyar Dalibai yan Karamar Hukumar Mairuwa (MALSU a lokacin akwai Mairuwa LG kafin aka koma tsohon tsari) , Hakimi ya bamu hadin Kai sosai muka dinga hada tarurrukan bita da wayar da kan matasa akan neman ilimi na addini da zamani. Hakan yayi matukar tasiri wajen samar da masu ilimi da yawa a yankin. A duk irin wadannan taruka da kuma shirin koyarwa na musamman da muka rinka yi (extra lessons), Hakimi ya taka rawa ainun da aljihunsa da kwarewar shi wajen ganin samun nasarar shirin . Sannan ya karfafa matasan akan samar da kungiyoyin taimakon kai da kai.

Har ila yau, a tsawon wannan shekaru 25 na mulkin Sarkin Rafi a Mairuwa , an samu karin ingancin dabarun noma tare da samun taimakon kungiyoyin bayar da agaji a harkar noma , kiwo da sana’oi. Ba zamu taba mantawa ba a lokacin shi ne aka kafa katafaren kamfanin nan na albarkatun gona da kiwo na West African Cotton Company (WACOT). Har yanzu muna cin gajiyar shi tare da wani kamfani na Sun Agro da sauran su a yankin Mairuwa.

Babban cigaba da wannan basarake ya kawo ma garin Mairuwa shine inganta zaman lafiya ta hanyar tabbatar da adalci tare da kawo sasanci a tsakanin al’umar shi a koda yaushe. Jama’ar Mairuwa shaida ne akan irin salon mulkin Sarkin Rafi na jawo jama’a a kusa da shi tare da nuna masu kauna, yayin da a lokaci guda yake tabbatar da tarbiya da bin doka da oda . Wannan kyawawan halaye na Sarkin Rafi sun kawo cigaban tattalin arziki da yalwa a tsakanin al’uma, sannan hakan ya haifar da samun alummar Gunduma masu hadin kai, biyayya ga hukuma da kaunar junan su.

A ranar 24 May 2021 daidai Maigirma Sarkin Rafi ya cika Shekaru 25 masu albarka a wannan aikin da Allah ya dora mashi na jagorancin Kasar Mairuwa.

Maigirma Sarkin Rafi Sani dan Sarkin Maska Idiris Sambo ne ,kuma jikan Sarkin Katsina Usman Nagogo ne domin shine ya haifi mahaifiyar shi, Hajiya Hussaina. Kuma kani ne ga Maigirma Sarkin Maskan Katsina Hakimin Funtua Alhaji Sambo Idris Sambo. An haife shi a shekarar 1961 inda ya fara karatun addini bayan da ya tasa kamar yadda yake a Kasar Hausa. Sannan ya halarci makarantun Primary zuwa Secondary a tsakanin shekarun 1967- 1982. Har ila yau ya halarci Hassan Usman Katsina Polytechnic inda ya karancin bangaren injiniya , daga bisani ya kama aiki da Katsina Steel Rolling Company Ltd inda ya kai matsayin babban ma’akaici. Yana wannan aiki ne Allah ya kaddara aka duba cancantar shi aka bashi Hakimcin Gundumar Mairuwa a ranar 24 May 1996. Aikin da yake yi bisa kokari da rikon amana har zuwa yanzu. Kasar Mairuwa tana da Dagatai guda 8, tayi iyaka da kasar Sarkin Yamma (Faskari), kasar Sarkin Maska(Funtua) ,kasar Makama(Bakori), Sarkin Pauwa(Kankara) da Yandoton Tsafe(Zamfara State). Sarkin Rafi na da iyali da zuriya.

Muna fatan Allah ubangiji ya kara ma Sarki lafiya da yawan kwanaki masu albarka . Allah ya sanya muga cikar shi Shekaru Hamsin a kan mulki har gaba da hakan cikin koshin lafiya da rufin asirin ubangiji. Ameen.

Aminu Mansur Mairuwa, Esq
Dokajin Magajin Garin Katsina

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Alleged Defamation: Gov. Masari demands N10bn, apology from journalists

Gov. Aminu Masari of Katsina State has demanded the payment of N10 billion as damages from Mr. Emmanuel Ogbeche and Mr. Ochaika Ugwu, Chairman...

Biliyan Ɗari shida da Miliyan ɗari biyu da Hamsin, Tallafi daga Gwamnatin Tarayya domin ɓunƙasa Karkara da gandun Daji a jihar Katsina…..

Biliyan Ɗari shida da Miliyan ɗari biyu da Hamsin, Tallafi daga Gwamnatin Tarayya domin ɓunƙasa Karkara da gandun Daji a jihar Katsina..... A ranar Alhamis...

DIRECTOR-GENERAL INAUGURATES NYSC MEGA PRINTING PRESS

NYSC Director-General, Major General Shuaibu lbrahim today inaugurated the NYSC Mega Printing Press in Kaduna. He said the project, which was conceived almost a decade...

Shugaba Buhari Ya Miƙa Ta’aziyyarsa Ga Iyayen Hanifa, Yarinyar Da Aka Kashe A Kano.

Daga Zaharaddeen Gandu Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjina wa 'yan sandan Jihar Kano game da gano wanda ake zargi da kashe Hanifa Abubakar mai...