Advert
Home Sashen Hausa SHEKARU BIYAR GA DUK MAI LUWADI KO MADIGO A KASAR GHANA.

SHEKARU BIYAR GA DUK MAI LUWADI KO MADIGO A KASAR GHANA.

Hassan Male @Katsina City News

Kwamitin Majalisar dokokin Ghana kan harkokin tsarin mulki da shari’ah ya fara zaman sauraron jin bahasi game da wani ƙudurin doka mai cike da ka-ce-na-ce kan haramta ayyukan ‘yan luwaɗi da maɗigo.

Ƙudurin dokar na neman ɗaure duk mutumin da aka kama da aikata luwaɗi da maɗigo tsawon shekara biyar a gidan yari, sai kuma ɗaurin shekara goma a gidan yari ga masu yayata ayyukan luwaɗi da maɗigo a ƙasar.

Kwamitin ya karɓi buƙatu fiye da 100 tun bayan kafa shi a watan Agustan bana.

Kudurin na ɗabi’un iyali ya haifar da mahawara a ƙasar inda ƙungiyoyi masu ɗa’awar kare ƴan luwaɗi da maɗigo da ke ganin ya saɓa dokar ƙasa.

Amma shugabannin adinin kirista a ƙasar na ganin kudirin ya yi daidai da zaɓin al’umma inda ɗauki ayyukan maɗigo da luwaɗi matsayin ‘babbar barazana ga al’adun Ghana.”

Fiye da rabin ƙasashen Afirka sun haramta luwaɗi kuma yawanci hukuncinsa kisa ne.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE FEDERAL MORTGAGE BANK OF NIGERIA (FMBN) HAS MADE HISTORY UNDER THE BUHARI ADMINISTRATION!

#PositiveFactsNG Do you know that ever since the Federal Mortgage Bank of Nigeria (FMBN) was established about 25 years ago, its greatest record of achievement...

YANZU-YANZU | Jirgin ruwan Bagwai dake jihar Kano mai dauke da fasinjoji 40 Yayi hatsari

Jirgin ruwan wanda ya debo dalibai mata da maza daga garin Badau zuwa garin Bagwai a jahar Kano yayi hatsari a cikin ruwan Yanzu...

ALLAH SARKI: ALLAH KA RABA MU DA RANAR NADAMA

Danjuma katsina  @Katsina City News A shekarar 2000 na dawo Katsina da zama, bayan shekaru na gwagwarmaya da tsallake siratsai kala-kala. Bayan na dawo na tsara...

Yadda Kotu Ta Ruguza Zaɓen Bangaren Ganduje Na Jam’iyyar APC

Wata babbar kotun Abuja ta soke zaben shugabannin jam'iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Alkalin kotun Hamza Muazu ya haramta zaben da...

EFCC Charges Corps Members To Take CDS More Seriously

The Port Harcourt Zonal Commander of the EFCC, Assistant Commander of the EFCC, ACE Aliyu Naibi has called on members of the National Youth...