Shekaru 38 Da Rasuwar Marigayi Malam Aminu Kano.

Daga Anas Saminu Ja’en

Shahararren ɗan siyasan a arewacin Najeriya, Marigayi Mallam Aminu Kano wanda ya riƙa fafutukar karɓowa talakawa ƴancin su, Ya rasu ne ranar 17 ga watan Afrilu 1983 a jihar Kano zamanin mulkin Alh. Shehu Aliyu Shagari yana mai shekara 62 a duniya.

Malam Aminu Kano yana tare da jam’iyyar NPC kafin ya ɓalle da jama’ar sa zuwa NEPU. Malam da mutanen sa sun gamu da tsangwama daga manyan NPC a NEPU, A 1954 yayi takarar kujerar majalisa ya sha ƙasa hannun Maitama Sule daga baya Aminu Kano samu zuwa majalisar.

Malam Aminu Kano yana cikin manya a majalisa a shekarar 1959. Bayan an kifar da gwamnatin su Sardauna kuma Malam ya riƙe Ministan lafiya na tsawon lokaci a gwamnatin Sojan ta Gowon. A 1978 Aminu Kano yayi takarar shugaban ƙasa amma jam’iyyar sa ta PRP ba ta kai labari ba, da shi akai ta gwagwarmaya wajen mayar da mulki ga hannun farar hula azamanin Yakubu Gawon wanda Yakubun ya daga bayar da mulkin wanda adalilin hakan ya haddasa hanbarar da gwamnatin Gawan din a shekarar 1975 inda Murtala Muhammad ya gajeshi.

Da shi aka yi gwagwarmaya wajen mayar da mulki ga farar hula a shekarar 1979. Malam Aminu Kano shi ne shugaban jam’iyar PRP kuma ɗan takararta na shugabancin ƙasa a shekarar 1979.

Ya yi ƙaurin suna wajen ƙin manufofin turawa dama duk wanda zai kawowa arewa wargi, mutum ne wanda bashi da kwaɗayi kuma baya siyasar kuɗi face aƙida zalla kawai, in dai ka jiyo muryar shi to a kan arewa ne da talakawa, duk ƙungiyoyin da ya yi ko ya jagoranta to gaba dayan su za a ji na Arewa ne.

Bayan mutuwar Marigayi Malam Aminu Kano an sakawa muhimman wurare sunansa kamar irin su filin jirgin sama na Kano wato Malam Aminu Kano Airport da kuma asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano wato Aminu Kano Teaching Hospital da sauran su da dama.

Anas Saminu Ja’en
17-4-2021

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here