Daga Comr Haidar Hasheem Kano

A rana irin ta yau 4 ga watan May 2002 jirgi mai dauke da tagwayen inji ƙirar BAC 1-11-500 wanda ƙasar Birtaniya ta ƙera ya yayi hatsari jim kaɗan da tashin domin ya nufi Jihar Lagos.

Hatsarin wanda yaci rayukan mutane 148 yayin da mutum 51 suka jikkata ciki har da ministan wasanni Ishaya Mark Aku na wancan lokacin akan hanyarsa ta zuwa Lagos ɗin domin kallon wasan sada zumunta tsakanin yan wasan Kenya da Najeriya.

Kamfanin jirgin EAS Airline ya bayyana cewa mutane hudu da suka tsira daga hatsarin akwai fasinjoji uku da kuma ma’aikacin jirgin guda ɗaya.

Hatsarin jirgin wanda ya sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da dimbin asarori da akayi ya zama mafi muni kuma abun tunawa a kowanne lokaci.

Shin ko da me kuke tuna wannan hatsarin jirgin?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here