Home Sashen Hausa Shekararre Ciki ( Post-Term Pregnancy)

Shekararre Ciki ( Post-Term Pregnancy)

Shekararre Ciki ( Post-Term Pregnancy)

Shekararre Ciki ( Post-Term Pregnancy)

Daga Siba Muhammad SKF

Kamar yadda aka sani yawancin juna biyu daga samuwarsa zuwa haihuwarsa, bai cika wuce sati 37 zuwa 42 ba. Amma wasu su kan wuce hakan wanda a turance ake kira da “Post-term ko past due” a Hausance kuma ace masa “shekarau”. Amma hakan na faruwa ne ga mataye kadan.

Me Ke Jawo Hakan?

Mace kan iya fuskantar yanayin wucewar lokacin haihuwarta ta dalilin wadannan abubuwa:

1. An sami kuskure wajen lissafi, inda wasu ke mance lissafinsu su rika de6e karshe har su fara tunane-tunane a kan sun wuce lokacin haihuwar wanda kuma ba hakan ba ne. Ana fara kirga ciki ne daga ranar da al’ada ta tsaya kamar yadda adadin kwanakin ya bambanta.

2. Idan mace ta kasance mai kiba/te6a (obesity).

3. Idan ciki ya zamanto shi ne na farko, ba ta ta6a haihuwa ba (primigravida).

4. Idan jaririn ya Kasance namiji ne. Wato akasari Maza ne kan wuce lokacinsu.

5. Idan an ta6a yi a baya, za a iya maimatawa.

6. idan ya kasance a dangi akwai wadanda suka ta6a yin hakan, to akwai yiwuwar wani ma ya samu.

7. Idan ya kasance mabiyiya ta sami matsala musamman dab da zuwan wata na 9 lokacin haihuwa, hakan kan sa yaron ya rasa abin da ya ke samu musamman karancin iska (Placental problem).

8. Yawwan shekaru, wato idan ya kasance mace na dab da barin haila gaba daya (menopause)

Shawarwari Da Kuma Abubuwan Da Ya Kamata A Yi.

1. Tun daga lokacin da aka sami juna biyu, ya kamata a ce mace tana samun kyakkyawar kulawar likita musamman masu haihuwar farko.

2. A daure a fara zuwa awo da zarar ciki ya kai wata Uku.

3. Yana da kyau mu mazaje mu tabbatar muna ba su kulawa tare da samar musu da hutu yadda ya kamata, inda hali a rage aikace-aikace.

4. Mu mazaje, mu rika raka matayenmu zuwa awo da kanmu, hakan zai rika sa su kara samun natsuwa.

5. Yawanci idan aka wuce sati 42 likitoci su kan yi binkice su yi (Ultrasound Scan) domin a tabbatar da lafiyar jaririn kalau, inda daga nan in aka ga lafiyar sa kalau a kan kara wa mace lokaci zuwa sati biyu a gani; inda daga nan in ba ta haihu ba, likita kan yanke shawarar tsokano haihuwar wato (inducing).

A. A kan yi “inducing” dinta ta hanyar yin wata allura a cikin jijiyar jini.

B. Sanya wani magani a gabanta (Inserting) domin gurin ya kasance ya yi taushi.

C. Ko kuma a yi aiki a ciro, in ya kasance yaron ya yi girma sosai ta yadda ba za ta iya haihuwar sa da kanta ba.

Allah ya taimaki iyayenm mata, mu kuma ya karfafe mu da daukar takalifinsu yadda ya kamata cikin yassarewarsa!

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here