Sheikh Zakzaky Ya Raba Kayan Abinci Ka Matan Kirista Da Suka Rasa Mazajen su A Kaduna

Sheikh Zakzaky Ya Raba Kayan Abinci Ka Matan Kirista Da Suka Rasa Mazajen su A Kaduna

Daga Bilya Hamza Dass

A cigaba da rabon kayan abinci da jagoran Harkar Musulunci a Najeriya Sheikh Ibraheem Zakzaky keyi a watan Ramadan wanda aka musu suna da ‘RAMADAN HADIYYA’ rabon ya isa ga Matan Kiristoci mazauna wani yanki na Kaduna, wanda suka rasa mazajen su da ake kira ‘widows’ a turance ko ‘Zaurawa’ a Hausance.

Anyi rabon ne ta hannun Pastor Yohana Buru, me ƙungiyar wanzar da zaman lafiya da sasantawa tsakanin addinai me suna ‘Peace Revival And Reconciliation Foundation Of Nigeria’ me babban Hedkwata a garin Kaduna. Wakilan Sheikh Zakzaky sun damka kayan gare shi inda ya miƙa su ga matan da suke da bukatar.

A lolaci guda, saƙon RAMADAN HADIYYA na Sheikh Zakzaky, ya isa ga ɗaruruwan Mabuƙata da suke garin Kaduna da ƙauyukan ta. Har walayau an kai saƙon ga mutanen da suke sansanin ƴan gudun Hijira na garuruwan Sokoto, dq Mafata Zamfara. Wannan de ba shi ne karon farko da Shehin Mallamin da ke tsare shekaru 6 yake wannan aikin ba. Ga wasu daga yanda akayi rabon.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here