Sheikh Gumi ya shiga daji yin da’awa

Fitaccen malamin addinin Islama Sheikh Ahmad Gumi ya ci gaba da shiga daji rugage yin wa’azi ga fulani makiyaya.

Wani shafin malamin na Facebook wanda ba a tantance ba ya nuna hotunansa a wata ruga yana wa’azi.

Shafin ya bayyana cewa Dr Ahmad Gumi ya yi wa’azin ne Rugar Malam Sule a dajin Chikuna a ranar Asabar.

Tun da farko wasu rahotanni a Najeriya sun ce malamin ya yi sasanci da wasu ƴan fashin daji ta hanyar wa’azinsa.

Rahotannin sun ce sama da ƴan fashi 500 suka amince su rungumi zaman lafiya a jihar Kaduna.

Social embed from facebook

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here