Sheikh Abduljabbar Kabara: Babbar kotun Kano ta amince da buƙatar malamin
BBC Hausa

Babbar kotun Kano da ke arewacin Najeriya ta amince da bukatar da lauyoyin Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara suka gabatar mata kan sauraren hujojinsu na neman soke umarnin wata kotun Majistire da ke jihar na rufe masallaci da makarantar malamin.

Alkalin kotun, Mai shari’a Nura Sagir ne ya bayar da umarnin, bayan la’akari da korafin da malamin ya yi na rashin ba shi damar kare kansa daga wasu zarge-zargen da ake yi masa.

A zaman kotun na ranar Laraba, babbar kotun ta bukaci karamar kotun majistiren da ta yanke hukuncin na baya da kuma malamin su dakata da daukar kowanne mataki har sai ta kammala yanke hukunci.

Mai magana da yawun kotunan jihar Kano Baba Jibo Ibrahim ya shaida wa BBC cewa a yanzu an tattara gaba daya an koma gaban babbar kotun ke nan, kuma za a saurari bukatar lauyoyin da malamin suka gabatar a ranar 27 ga watan Yulin nan.

BBC ta yi kokarin jin ta bakin lauyoyin Sheikh Abduljabbar Kabara, sai dai sun ce ba za su ce komai ba sai nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here