A Yau Litanin Wanda Yayi Dai~Dai Da 03/05/2021. Tsohon Dantakarar Sanatan Funtua Zone A Zaben Da Ya Gabata Na Shekarar 2019, Hon. Shehu Inuwa Imam Ya Ziyarci Babbar Sakatariyar PDP Dake Cikin Birnin Katsina.

Inda Ya Ziyarci Sakatariyar Jam’iyyar Domin Bayyyan Aniyar Shi Ta Tsayawa Takarar Gwamnan Jihar Katsina A Jam’iyyar PDP, Idan Allah Yakaimu Zaben 2023.

Hon. Imam Ya Tara Ciyamomin Party Na Jam’iyyar PDP Dake Kananan Hukumomin Jihar Katsina Guda Talatin Da Hudu (34 L.g). Tare Da State Working Committee Na Jam’iyyar PDP.

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP Na Jihar Katsina, Hon. Salisu Uli Shi Ne Ya Karbi Babban Bakon A Madadin Shugaban Jam’iyyar PDP Na Jihar Katsina, Hon. Salisu Yusuf Majigiri (Garkuwan Gabas).

Hon. Shehu Inuwa Imam Yayi Alkawarin Kawo Gyara Da Cigaban Jihar Katsina Idan Har Allah Ya Bashi Damar Zama Gwamnan Jihar Katsina A Lokacin Da Yake Jawabi.

Kuma Ya Bayyana Cewa Tsayawar Shi Neman Takarar Gwamnan Jihar Katsina Ya Samu Nasaba Ne Da Irin Yadda Al’ummar Jihar Katsina Da Masu Kishin Jam’iyyar PDP Suka Taso Shi Gaba Akan Cewa Ya Dace Ya Tsaya Wannan Takara Domin Ceto Jihar Katsina Daga Halin Da Ta Tsinci Kanta A Ciki. Tun Daga Abinda Ya Shafi Rashin Tsaro, Rashin Aikin Yi, Rashin Gudanar Da Ayyukan Raya Kasa, Da Sauran Matsaloli Iri Daban~Daban Dake Cikin Wannan Gwamnati Ta APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here