Shawarwari 6 da Gwamna Zulum ya baiwa Buhari a yau idan yana so ya kawo ƙarshen Boko Haram

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya zayyano shawarwari guda 6 da yake so shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aiwatar da su idan yana son ya kawo ƙarshen rikicin Boko Haram da ya addabi yankin arewa maso gabas.

Zulum ya yi wannan tsokaci ne yayin da tawagar shugaban ƙasa karkashin jagorancin shugaban majalisar dattawa, Dakta Ahmed Lawan ta ziyarce shi a yau Litinin a Maiduguri akmar yadda wata sanarwa da kakakin Gwamnan, Abdulrahman Ahmad Bundi ya fitar.

Sanarwar ta ce tawagar a madadin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da gwamnatin tarayya, ta je Maiduguri ne domin jaje da kuma ta’aziyya ga ƴan uwan waɗanda ƴan Boko Haram suka kashe a Zabarmeri da kuma al’ummar jihar Borno.

Shawarwarin su ne;

1. Tabbatar da ɗaukar matasan Borno cikin sojoji don tallafawa sojoji nan take.

2.Tabbatar da aikin hadin gwiwa da sojoji daga makwabta Chadi, Nijar da Kamaru wajen kakkabe ragowar ƴan Boko Haram dake Tafkin Chadi.

3. Samar da kayan aikin zamani domin share dajin Sambisa.

4. Samarwa dakaru Sojoji motocin yaƙi na zamani da ma sauran jami’an tsaro.

5. Tallafawa gwamnatin jihar wajen dawo da ‘yan gudun hijirar da ke kasashen Nijar da Kamaru.

6. Karawa mutanen Barno hanyoyin samun ingantataccen rayuwa.

Daga ƙarshe Farfesa Zulum ya ce idan shugaban ƙasa ya aiwatar da waɗannan shawarwarin zai taimaka wurin kawo ƙarshen rikicin Boko Haram da aka shafe shekara 11 yana addabar yankin Arewa maso Gabas.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here