SHARI’AR MAHADI; YAU KOTU TA ZAUNA
Ahmad Muhammad
@ katsina city news
A yau Litinin 16/11/2020 aka ci gaba da zaman sauraron shari’ar Alhaji Mahadi Shehu, dan Katsina mazaunin Kaduna da ke kwarmata zarge-zarge a kan gwamnatin Jihar Katsina da wasu mukarrabanta.
A zaman na yau, Lauyan gwamnatin Jihar Katsina, Barista Anest Obadineke, ya ba da hujjoji a takardu masu shafuka 16 cewa, kotun na da hurumin sauraren karar da suka shigar a kan Alhaji Mahadi Shehu.
Lauyan wanda ake zargi, Barista Anjob, ya bayyana cewa, tunda yanzu suka karbi hujjojin da Barista Obadineke ya bayar, suna bukatar lokaci su yi nazarinsu, kuma su ba da amsa a kai.
A kan haka Alkalin kotun ta Majisirate I, Mai Shari’a Abdu Ladan, ya dage zaman kotun zuwa ranar Talata 8 ga watan Disamba na wannan shekarar domin ci gaba da sauraren hujjojin Lauyoyin Mahadi a kan cewa kotun ba ta da hurumin sauraron karar da aka shigar.
Gwamnatin Jihar Katsina ce ta hannun Kwamishinan Shari’a na Jihar, Barista Ahmad Elmarzuq ce ta shigar da kara a kotun a kan Mahadi Shehu bisa zargin yana kokarin tunzura jama’ar Katsina su kyamaci gwamnati, kuma suna zargin ya mallaki wasu takardun bogi a kan gwamnatin ta Katsina.
A zaman farko na wannnan shari’ar, Lauyoyin Mahadi sun yi korafin cewa kotun ba ta da hurumin sauraren wannan shari’ar, kuma suka nemi a dakatar da duk wani yunkurin kama wanda ake zargin wato Mahadi Shehu.
A zaman yau Lauyan da ke wakiltar gwamnatin Katsina, ya kawo hujjojinsa a rubuce na cewa kotu na da hurumi. Ya ce a zama na gaba za a ji hujjojin Lauyoyin Mahadi Shehu, sai Alkali ya dau matsaya bisa hujjar da ya gamsu da ita, sai ya yanke hukunci a kai.
________________________________________________
Katsina City News na bisa yanar gizo na www.katsinacitynews.com. Kuma page Katsina City News, kana kuma iya zama memba na group din Katsina City News duk a Facebook.
Muna a kan Twitter, You tube da Instagram.
Duk sako a aika ga 07043777779