Advert
Home Sashen Hausa Shaikh Zakzaky Ya maka Hukumar DSS Da babban Lauyan Gwamnati Kotu Kan...

Shaikh Zakzaky Ya maka Hukumar DSS Da babban Lauyan Gwamnati Kotu Kan Riƙe Musu Fasfo, Ya Nemi A Biyasu Diyya….

Shaikh Zakzaky Ya maka Hukumar DSS Da babban Lauyan Gwamnati Kotu Kan Riƙe Musu Fasfo, Ya Nemi A Biyasu Diyyan Naira Biliyan 2

Ƙarar wacce ofishin babban Lauya me zaman kan shi kuma, me kare hakkin Bil’adama Mr. Femi Falana (SAN) ya gabatar, Shaikh Zakzaky na neman abubuwa guda bakwai, ciki da kotun ta umarci wadanda ake karar su su biya diyyar Naira Biliyan Biyu a dukkan matsayin da misali kan abin da ya faru na take masu dukkan hakkokin su na walwala da ƴanci, da kuma lalata musu kadarori.

Sheikh Zakzaky, ya nemi kotun ta umurci waɗanda ake ƙara da su basu takardun tafiye-tafiyen (Fasfot) tare da mai dakin sa mai lamba A50578740 wanda suka kwace tun daga watan Mayun 2019, wanda hakan ya sabawa kundin tsarin mulki, kuma take musu hakkokin su ne na ‘yancin walwala wanda kaitsaye ya saɓa da sashi na 41 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya, 1999, da Mataki na 12 na Dokar ‘Yancin Dan Adam da Jama’a (CAP A9), Dokokin Tarayyar Najeriya, 2004.

Shaikh Ibraheem Zakzaky, yana son kotu ta bayyana cewa kin DSS da AGF na ba shi damar tafiya kasashen waje don neman magani ya zama barazana ga rayuwarsa kamar yadda sashe na 33 na kundin tsarin mulkin 1999 ya tabbatar. Zakzaky ya roki kotun da ta bayar da umarnin da zai hana wadanda ake kara kara take hakkin sa.

—Bilya Hamza Dass, a fassaran rahoton Punch

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE FEDERAL MORTGAGE BANK OF NIGERIA (FMBN) HAS MADE HISTORY UNDER THE BUHARI ADMINISTRATION!

#PositiveFactsNG Do you know that ever since the Federal Mortgage Bank of Nigeria (FMBN) was established about 25 years ago, its greatest record of achievement...

YANZU-YANZU | Jirgin ruwan Bagwai dake jihar Kano mai dauke da fasinjoji 40 Yayi hatsari

Jirgin ruwan wanda ya debo dalibai mata da maza daga garin Badau zuwa garin Bagwai a jahar Kano yayi hatsari a cikin ruwan Yanzu...

ALLAH SARKI: ALLAH KA RABA MU DA RANAR NADAMA

Danjuma katsina  @Katsina City News A shekarar 2000 na dawo Katsina da zama, bayan shekaru na gwagwarmaya da tsallake siratsai kala-kala. Bayan na dawo na tsara...

Yadda Kotu Ta Ruguza Zaɓen Bangaren Ganduje Na Jam’iyyar APC

Wata babbar kotun Abuja ta soke zaben shugabannin jam'iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Alkalin kotun Hamza Muazu ya haramta zaben da...

EFCC Charges Corps Members To Take CDS More Seriously

The Port Harcourt Zonal Commander of the EFCC, Assistant Commander of the EFCC, ACE Aliyu Naibi has called on members of the National Youth...