Saudiyya ta jaddada wa Jamus yin Allah wadai da ɓatanci ga Annabi

Sarki Salman na Saudiyya ya tabbatar da matsayin masarautar na yin Allah wadai da zanen ɓatanci da aka yi wa Annabi Muhammad a Faransa.
Jaridar Arab News ta ce Sarkin na Saudiyya ya jaddada matsayin ƙasar ne yayin tattaunawa da shugabar Jamus Angela Merkel.
Shugabannin biyu sun tattauna ne a taron G20 na ƙasashe 20 masu ƙarfin tattalin arzikin duniya wanda ya mayar da hankali kan yaƙi da ta’addanci da kuma inganta hulɗa.
Sarki Salman yayin tattaunawar ta wayar tarho da Angela Merkel ya kuma jaddada muhimmancin ƴancin faɗar albarkacin baki wanda ya ce ya kamata ya kasance wani kyakkyawan ɗabi’u wanda zai tabbatar da girmamawa da kuma zaman tare, amma ba wata hanyar yaɗa ƙiyayya ba.