Gwamnatin Saudi Arabiya ta bi sahun wasu kasashen duniya wajen hana jiragen sama da suka tashi daga Najeriya shiga kasar sakamakon samun wasu mutanen dake dauke da sabon nau’in cutar korona da ake kira Omicron.

Rahotanni daga birnin Kano sun ce yanzu haka maniyata Umrah da dama sun makale a birnin sakamakon wannan mataki da Saudiyar ta dauka, yayin da jami’an kula da tashohin jiragen saman Malam Aminu Kano suka tabbatar da samun umurnin hana jirage tashi zuwa kasar.

Wata matafiya da yanzu haka take birnin Kano akan hanyar ta na zuwa Umrah a kasar ta Saudiya ta shaidawa RFI Hausa cewar tabbas an sanar da su cewar gwamnatin Saudiya ta soke tafiyar su daga Najeriya.

Majiyar Blueink News Hausa, Jaridar Daily Trust ta jiyo ta bakin wani jami’in ofishin Jakadancin Saudiyar dake Kano na cewar tabbas sun samu umurnin hana jiragen sama daga Najeriya tafiya kasar.

Sai dai Jaridar ta ruwaito cewar duk da wannan umurnin, wani babban jami’in kamfanin jiragen sama ya shaida mata cewar jirage biyu sun tashi yau da safe daga Abuja zuwa Jeddah wadanda suka hada da Qatar Air da Badar Air.

Gwamnatin Najeriya ta bakin ministan yada labarai Lai Mohammed ta bayyana bacin ran ta da irin wannan mataki da kasar Birtaniya da kuma Canada suka dauka na hana baki daga Najeriya zuwa kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here