Sau Talatin naje Makka da sana’ar Daukar Hoto……. Alhaji Abashe Kofar Guga…

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News

A garin Katsina, da wasu jihohi makwafta sunan Alhaji Abashe Mai Hoto, ba ɓoyayya bane, musamman ga masu sauraren wakokin Dakta Mamman Shata Katsina,

Alhaji Abashe mai Hoto, shine Mutum na farko Bahaushe a ƙasar Katsina da ya fara sana’ar Daukar Hoto, Inda ya kwashe Shekaru Hamsin da biyar a akan sana’ar tun a shekarar 1966, zuwa yanzu, kamar yanda Jaridun Katsina City News, ta zanta dashi:

“Ni sunana Abashe, an haifeni Unguwar Kofar Guga a garin Katsina, tun tasowata dai na fara karatun addini, a nan Unguwar tamu, daga nan aka kaini Zariya wajen karatu, a zamanin Sarki Jafaru, bayan nayi karatu, ina nan, kuma daga Zariya akwai wani yaya na da muke taɓa Kasuwanci, a tare, amma ba na zama waje guda ba, muna yawo garuruwa, Irin su kagoro, Naija, Jos, da Kogi, dayake banyi, karatun Zamani ba, sai yace yakamata in dogara da kaina, wace sana’a nafi so…? sai yasa a koya mani. Sai nace mashi, sana’ar daukar Hoto, sai yace wannan sana’ar bata Hausawa bace, indai canza wata, to nidai dayake abinda nafi so, kenan sai na fahimtar dashi, kuma nace masa, zan taimaki Al’uma ta wannan sana’ar ko ba komai ba Hausawa ke yinta ba, kuma yanzu zamani yazo komi sai da Hoto, ko Makka zaka sai ammaka Hoto.

Sai ya aminta da haka, ya daukeni ya kaini a Jos, aka kaini Makaranta koyon Aikin na Hoto. To aƙa’idan karatun shekara biyu ne, amma dayake ina son Karatun, sai na maida hankali, cikin Ikon Allah a wata tara, na kammala kuma akabani sakamako (Certificate) na dawo, Yayana ya saimun kyamarori, da kayan aiki, sosai na shigo Katsina dasu, na fara aikin Hoto, alokacin nan Katsina Mutum biyu ne Inyamurai ke Hoto, kuma suma sunji tsoro sun bar garin saboda ba’adade da yin rikicin Biyafara ba, sai yazamana a ‘yan Kasuwa, ba na Gwamnati ba, nine Bahaushe na farko a Katsina daya fara sana’ar Hoto.

Lallai munga nasara da ci gaba sosai, a rayuwa a cikin wannan sana’ar, tsawon shekaru Hamsin da biyar, naje Makka sau Talatin, tsawon shekarun nan bantaba Babbar Sallah a gida ba, Har ta kaiga ina sha’awar inga nayi Babbar Sallah a gida.

Ban dakata da zuwa Makka ba sai a lokacin, da Mangal yazo (Max air) yazo, shima Ita Mahaifiyar Mangal din taƙi yarda, saboda tace, babu wanda take so yayimata Hoto, a Makka sai ni, haka dai mukayi ta gungurawa cikin Nasara,nidai tunda na fara wannan sana’ar ban taba ganin ci baya ba, zuwana Makka na farko, Alokacin sa’idu barda yana shugaban Hukumar Al’zai ta ƙasa, kamar shekarar 1977, yabani Kujera bayan da nayi mashi Hotunan Bikin diyar shi.

Alaƙata da shata, shima Hoto, ya haɗa mu, wata rana shata……..

Jaridar Katsina City News sun Tattauna dashi, a cikin Faifan bidiyo, mai tsawon Mintina 27, mun kasa Bidiyon kashi, biyu, domin ji da ganin Tattaunawar kamar yanda take, sai ku duba YouTube channel na Katsina City News TV, zakuji daga bakinsa, wannan tsakuro maku mukayi.

Katsina City News na busa yanar gizo a www.katsinacitynews.com ko ku sauke Manhajar mu ta Katsina City News daga Playstor a wayoyin ku……………………………………………………………….☎️07043777779

YouTube KATSINA CITY NEWS TV

Facebook: Katsina City News

Twitter: @Katsinacitynews

Insgram: Katsinacitynews

Whatsapp: 07043777779/08036342932

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here