Advert
Home Sashen Hausa SATAR DUKIYAR AL'UMA A UNGUWAR KOFAR KAURA INDA AKE GINA TITIN ƘARƘASHIN...

SATAR DUKIYAR AL’UMA A UNGUWAR KOFAR KAURA INDA AKE GINA TITIN ƘARƘASHIN ƘASA A KATSINA…. Laifin Gwamnati ko Kamfanin da ke Kwangilar aikin…?

SATAR DUKIYAR AL’UMA A UNGUWAR KOFAR KAURA INDA AKE GINA TITIN ƘARƘASHIN ƘASA A KATSINA…. Laifin Gwamnati ko Kamfanin da ke Kwangilar aikin…?

Zaharaddeen Ishaq Abubakar@Katsina City News

A ranar Alhamis 23 ga watan 11 na 2021 Gwamnan Katsina Rt.Hon Aminu Bello Masari ya kaddamar da wasu Manyan Ayyukan ci gaba a Babban Birnin Katsina, inda aka fara gina Titunan Ƙarƙashin ƙasa a Unguwar Kofar Kaura da Kofar Kwaya duk acikin Birnin Katsina, Kamfanin TRACTA ne Kamfanin da ya amshi kwangilar, Amma tun daga ranar da aka sanya ɗan ba, na fara wannan muhimman Ayyuka sai Unguwar ta kasa samun tsaron da ya dace, Inda matasa daga ko ina, a yankin Unguwar suka dunga ɓarkowa suna satar kayan Gwamnati da na Al’uma.

Ankasa fita haƙƙin makwafta masu sana’a awajen inda dayawa daga Makwafta suka tabbara da babu wani wanda ya tuntuɓe su, ko yace kwashe kayanka, Hukumar Nefa bata iya zuwa wajen ta duba yanayin wuta da yanda aikin zai iya shafar wutar lantarki dake titin ba, Jami’an tsaro da aka iya kawowa a nan, mafiya yawansu ‘Yan sa kaine da ‘yan unguwa…. wadanda basa iya hana ɓarayi kwasar kayan mutane,  Shin dama a ƙa’ida idan za’afara aiki da zai shafi Al’uma  kai tsaye kuma cikin mutane, haka ya dace afara batare da lura da haƙƙin Al’uma ba…? Shin yadace Kamfanin da ke Wannan Kwangila da kuma Gwamnati su sanya Ido a dunga ɓannata Dukiya da satar kayan mutane…? Wake da Haƙƙin Kula da Lafiya da Dukiyar Al’uma…? Aikin da zai dauki tsawon Shekara ana yinsa shin sakaci da tsaro ya dace a Unguwa Irin wannan…?muna fatan Gwamnati da Kamfanin dake wannan Kwangila zasu ɗauki matakin da ya dace domin kare Dukiyar jama’a, kada jama’a su kaiga neman Haƙƙinsu a Kotu….

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Jam’iyyar PDP a Katsina ta sanar da kuɗin form ɗin takarar shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli a zaɓe mai zuwa

Jam'iyyar PDP a Katsina ta sanar da kuɗin form ɗin takarar shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli a zaɓe mai zuwa Babbar jam'iyyar adawa a jihar...

Aisha Buhari Ta Naɗa Kashim Shettima A Matsayin Shugaban Kwamitin Amintattu Na Kwalejin Future Assured

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, ta naɗa Kashim Shettima, tsohon gwamnan Jihar Borno, a matsayin shugaban kwamitin amintattu na Kwalejin Future Assured da ke...

WHICH PARTS OF NIGERIA ATTRACTED MORE FOREIGN INVESTMENTS IN THE YEAR 2021?

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/262020019347856/

AGAIN, A NEW ADDITION TO NIGERIA’S MARITIME SECURITY VESSELS!

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/261866049363253/

Jami’an Hukumar yaƙi da yima Tattalin Arzikin ƙasa Ta’annuti ta ICPC sunyi Dirar Mikiya jihar Katsina….

Jami'an Hukumar sun gano yadda akayi Haɗin baki da Ɗan Majalisar Wakilai da kuma Mai duba ƙwangila aka sace kuɗin ƙwangilar Naira Milyan Talatin...