..fassarar Rahoton London Times
Aliyu Sale @Katsina City News
Jaridar Times da ke fitowa kullum-kullum a Birtaniya, ta ba da labarin cewa, Sinawa da
ke hakar ma’adinai a Nijeriya suna ba da makudan kudade ga kungiyoyin ’yan ta’adda
domin su ba su damar shiga kowanne lungun kasar suna hakar ma’adinai ba tare da
wata matsala ba.
A wani bincike da kungiyar bin diddigin al’’amura ta SBM da ke birnin Lagos ta aika wa jaridar Times, ya nuna wasu hotunan bidiyo a shafukan sada zumunta irin na WhatsApp
na wasu shugabannin ’yan ta’adda suna shan alwashin cewa dole ne duk wasu ma’aikatan China da ke son fara aikin hakar ma’adanai a yankunansu, su biya su haraji.
Rahoto da jaridar Times ta Birtaniya ta wallafa ranar 15 ga watan Afrilu mai taken “Beijing na tallafa wa ayyukan ta’addanci a kaikaice” a Nijeriya, ya tabbatar da cewa China na karfafa ayyukan ta’addanci a Afrika ta hanyar ba ’yan ta’addan makudan
kudade.
Rahoton ya yi bayanin cewa, ’yan kasar China da ke hakar ma’adinai a Zamfara bisa doka, suna kuma zama a matsayin wadanda ’yan ta’adda ke amfani da su wajen samun kudaden fitar hankali a Jihar da wasu jihohin Arewa maso Yammacin Nijeriya da kuma wasu sassan kasar.
“Kamfanonin China da ke aiki a Nijeriya sun shiga wata yarjejeniya da ’yan ta’adda domin kada a kai wa mutanensu hari,” a cewar jaridar Times.
A cewar rahoton, ’yan kasar China da suka kai su dubu 100 zuwa dubu 200 na fuskantar hare-hare a ’yan shekarun nan da rikici ya yi kamari a Nijeriya.
“Wani bincike da kungiyar bin diddigin al’amura ta SBM da ke birnin Lagos suka aika wa jaridar ta Times da ke Birtaniya, wanda ya nuna yadda wasu faya-fayen bidiyo na shugabannin ’yan ta’addar da ke yawo a kafafen sada zumunta na zamani, musamman
WhatsApp, yana nuna yadda karfin ’yan ta’addar yake, inda suke nuna muddun Sinawa na son zuwa yankunan da suke da iko da shi domin hakar ma’adinai, to dole ne su biya su harajin yin haka.
’Yan ta’addan dai sun mamaye Arewa maso Yammacin kasar, tare
da mayar da yankin wajen zubar da jini.
“A daya daga cikin kunshin rahotannin a Zamfara, masu binciken sun yi tozali da wani
bidiyo da ya karade Nijeriya da wasu daga cikin ’yan ta’addan da ke da iko da wani wajen hakar ma’adanai da Sinawan ke aikin hakar zinare da kuza suke
bayyana matsayinsu a kan kudaden da suke so a ba su kafin su amince su yi aikin hakar ma’adanai a yankin,” in ji rahoton.
Jaridar Times, kamar yadda TheCable ta ruwaito, ta ce ban da wannan ma, ’yan
kwangilar hakar ma’adinai Sinawa suna biyan masu hakar ma’adinai ’yan kudi kalilan, kana su kwashe ma’adinan suna fita da su kasar ta haramtacciyar hanya, duk da yake
wadansu lokuta ana kama irin wadannan Sinawan.
“A shekara ta 2020, masu hakar ma’adinai 27 da aka kama a Jihar Osun akwai Sinawa 17 cikin su. Haka ma a watan Oktoba na bara an daure wani Dan China da ake kira
Gang Deng, mai shekaru 29, na tsawon shekaru biyar, bayan samun sa da ton 25 na wani ma’adini da ake amfani da shi wajen kera baturan mota.
“Sannan ban da wannan ma, SBM sun ba da labarin cewa, an sami Sinawa da hannu
dumu-dumu a rikicin Boko Haram a Arewa maso Gabashin Nijeriya, inda suke fasakwabrin bakin karfe zuwa wajen kasar nan ana biyan su,” kamar yadda jaridar ta
bayyana.
Jaridar HumanAngle da ke fitowa a Intanet a Nijeriya, ita ma ta ba da rahoton cewa masu
aikin hakar ma’adinai a yankin Arewa maso Yamma suna biyan ’yan fashin daji harajin
kashi 10% na abin da suke samu duk wata.
Sai dai tuni Gwamnatin China ta musanta wadannan zarge-zargen na cewa tana biyan
’yan ta’adda cin hanci don samun damar shiga wuraren ayyukan hakar ma’adanai a Nijeriya.
China ta ce ba za ta taba sa hannu a cikin duk wani abu da ya danganci tallafa wa ayyukan ta’addanci ba.
A sanarwa da ofishin jakadancin China da ke Nijeriya ya fitar, ta bayyana rahoton a
matsayin “maras kan gado,” tare da nuna rashin jin dadin gwamnatin kasar kan wannan rahoto.
“Zarge-zargen da ke kunshe a rahoton ba su da wani tushe balle makama, kuma akwai
ayar tambaya game da rahoton.
“Gwamnatin China da ma ofishin jakadancin China a Nijeriya, ko da yaushe suna karfafa gwiwa, tare da yin kira ga kamfanonin China da ’yan kasar da ke zaune a Nijeriya su kasance masu bin doka da oda,” in ji sanarwar.
Ofishin jakadancin China a Nijeriya dai ya jaddada cewa a tsawon shekaru da dama, dangantaka tsakanin China da Nijeriya ta taimaka wajen bunkasa ci gaba mai amfani ga duk kasashen biyu da al’ummominsu.
“Don haka za mu ci gaba da aiki da gwamnatin Nijeriya don tabbatar da ci gaban kasar da shawo kan matsalolin tsaro.
“Muna kuma maraba da abokan hulda na duniya, su shigo cikin wannan yunkuri, amma za mu yi watsi da duk wata aniya ko matakin da zai gurbata alakarmu,” in ji sanarwar.