Zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya isa Fatakwal babban birnin jihar Rivers a wata ziyarar kwana biyu da ya kai jihar.
Tinubu ya je jihar ne domin ƙaddamar da wasu ayyukan da gwamnan jihar Nyesom Wike ya gudanar.
Ayyukan da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar zai ƙaddamar sun haɗar da gadar samar da ginin kotun majistare.
Mista Wike tare da muƙarraban gwamnatinsa ne suka tarbi zaɓaɓɓen shugaban ƙasar a lokacin da ya sauka a filin jirgin saman birnin fatakwal.
Ɗaruruwan magoya bayan Tinubu da Wike ne suka taru domin yi wa zaɓaɓɓen shugaban ƙasar tarba.
Tuni gwamna Wike ya ayyana ranar ziyarar a matsayin ranar hutu ga ma’aikata a faɗin jihar domin bai wa al’umma damar tarbar zaɓaɓɓen shugaban ƙasar.