Rundunar Yansandan jahar Katsina ta kaddamar da bada cakin kudi ga iyalai 21 na jami’anta da suka rasa rayukansu a yayi gudanar da aikinsu.
Mai rikon kujerar kwamishinan Yansandan jihar, mataimakin kwamishina DCP Shettima MD ne ya mika cakin kudaden ga iyalan Yansandan a ranar Alhamis din nan a takin taro na rundunar da ke Katsina.
MD, jim kadan bayan kammala mika cakin kudin ya ja hankalin iyalan da su yi amfani da kudin ta hanyar da ya dace.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Katsina da su kara bai wa jami’ansu hadin kai domin kawar da matsalar ta’addanci da ta addabi jihar.
A karshe ya yaba wa shugaban Yansandan na kasa wato IGP Alkali Usman Baba bisa kawo shirin tallafa wa iyalan Yansandan da suka mutu a wajen aiki.