Yana da wahala a tarihin siyasar Najeriya ,a samu wani dan siyasa da ya iya kowa kamar gwamnan jihar Katsina,Rt. Hon. Aminu Bello Masari, CFR.
“Sakaina uwar iya ruwa”. Ya iya malaman addini. Sai da ta kai babu wani Masallacin Jumma’a kona Khamsin Salawati da wani zai mike ya ce ba ai kaza da kaza ba, balantana mummunar addu’a.
Ya iya ma’aikatan gwamnati ,akwai lokacin da na ji daya daga cikin shugabannin kungiyar kwadago yana godiya, saboda biyan hakkokin ma’aikata, musamman albashi, kan kari.
Gwamna Masari aminin ‘yan jarida. Ban tsammanin akwai gwamnan da kungiyar ‘Yanjaridu ta ba kambunan girmamawa iri-iri a lokutta daban-daban kamar gwamna Masari. Kambu na karshe da ya amsa daga wurinsu,shugaban ‘yanjarida na kasa bakidaya ya zo da kan shi ya bada.
Ya iya ‘yan farar hula. Gwamna Masari ne gwamna na farko da ya dauko dan farar hula ya bashi babban mukami a gwamnati.Yana kuma da wuya yai kwamiti bai sanya Wakilin ” ‘yan-sa-ido ba”. Sannan ya bude kofa gare su da ya ba su dama su tunkare shi ga duk wani abin da ya shige masu duhu.
Gwamna Masari Na ‘Yan Adawa: A cikin salon shugabancinshi na tafiya da kowa,sai da ta kai,jihar Katsina babu wata adawa ta gaskiya. Bugun karshe da yai masu,shi ne lokacin zaben 2023.Da aka juya,aka juya,akai wata ranwa irin ta siyasa ,har yanzu masu sharhi akan siyasa sun kasa fashin baki daidai.
APC AKIDA: Lokacin da aka huro wutar cikin gida,duk an dauka za ta dore,ashe wutar kara ce. Yanzu ko tokar ba a san ya akai da ita ba.
Gwamna Masari na masarauta: Sabanin wani gwamna da yaso yai fada da sarki,gwamna Masari bai bi wannan tsarin ba.
Gwamna Masari Na fadar shugaban kasa: Duk jihar da shugaban kasa ya fito,sai ka samu gogaggen gwamna mai Kai zucciya nesa ,in ba haka ba kuwa,sai a gan su a shafin jarida.
Baya da hushi kamar Nasir El-rufa’i sannan baida wauta kamar Yahaya Bello,sannan bai cika shisshigi ba kamar Bagudu,bai kuma da cika-baki irin na Badaru.
NASARORI: Gwamna Masari ya zo da kundi mai suna Restoration Plan ,inda zai ba Ilimi,Noma,kiwon lafiya,ayyukan gine-gine da sauran su muhimmanci.
Gwamnatinshi ta yi kokari wurin gyara makarantu,gina sabbi,daukar malamai,gyara asibitoci,gina hanyoyi ,gadoji da sauran su.
KALUBALE: Gwamna Aminu Bello Masari ya fuskanci kalubale a mulki. Na farko shi ne kalubalen tsaro,na biyu masassarar tattalin arziki guda 2,na uku ya ki tsawata ma wasu jami’an gwamnatinshi. Na hudu, Matasa da Mata basu samu isashen wakilci a majalisar zartarwarshi ba. Na biyar rashin aiwatar da wasu muhimman tsare-tsare kamar sanya ma dokar masu bukata ta musamman hannu,kafa hukumar yaki da cin hanci da karbar korafe-korafe ,OGP,da sauran su.