Gobe take Sallah a Saudiyya.
Gwamnatin Saudiyya ta ce a gobe Juma’a za a gudanar da Idin Sallah karama sakamakon ganin jaririn watan Shawwal da aka yi a wannan Alhamis din.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shafin masallacin Harami na Makka da Madinah ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Shafin na Haramain Info ya ce an ga jaririn watan Shawwal yammacin wannan Alhamis din bayan duban tsanaki.
Ana dai fara duban watan Shawwal ne a yayin da watan Azumin Ramadana ke cika 29 galibi, a wasu lokutan kuma idan ya kai kwana 30.
Wannan na zuwa ne kwana biyu bayan da aka samu rabuwar kai a tsakanin masana ilimin taurari dangane da ganin jinjirin sabon watan.