Shugaban kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Air Peace a Najeriya Allen Onyema, ya ce kamfanin a shirye yake kwaso ‘yan Najeriyar da suka maƙale a ƙasar Sudan a kyauta, yayin da faɗa tsakanin rundunonin tsaron ƙasar ke ci gaba da zafafa a birnin Khartoum.
Sudan ta faɗa rikici tun ranar 15 ga watan Afrilu yayin da manyan rundunonin tsaron ƙasar da ke adawa da juna ke gwambza yaƙi da juna a ƙoƙarinsu na ƙarbe iko da Khartoum babban birnin ƙasar, da kuma yankin Darfur.
Mista Onyema ya ce a shirye kamfaninsa yake ya taimaka, saboda a cewarsa Najeriya ba za ta so ta rasa mutum guda daga cikin ‘yan ƙasarta da ke Sudan ba.
Ya ƙara da cewa yana da muradin taimakawa wajen ceto ‘yan Najeriyar da suka maƙale a Sudan, domin mayar da su ƙasar cikin kwanciyar hankali.
Yayin da rikicin ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 400, tuni ƙasashen duniya irinsu Amurka da Jamus da Faransa da Netherlands suka fara kwashe ‘yan ƙasashensu.
Tuni dai ɗaliban Najeriya da ke Sudan suka fara kiraye-kirayen a kwashe su daga ƙasar sakamakon rikicin da ke ci gaba da ruruwa ƙasar