Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News

Injiniya Bala Almu Banye (Zarman Katsina) a wajen ƙidayar gwaji garin Daura ta jihar Katsina
Hukumar Ƙidaya ta ƙasa NPC ta bayyana cewa babu batun tambaya akan Addini da wasu suke bayyanawa a matsayin “tambayar Addinin ka na ɗaya daga cikin tambayoyin da za’aiwa mutum alokacin ƙidayar.”
hukumar tace ba gaskiya bane, Jita-jita ne kawai.
hukumar ta saki wata takarda mai dauke da tsare-tsaren da kuma ire-iren tambayoyi da za’aiwa ‘yan ƙasa a lokacin gudanar da ƙididdigar.
Idan ba’amantaba a watannin da suka gabata hukumar ta NPC ta gudanar da ƙidaya ta Gwaji a wasu jihohi na Najeriya, daga ƙananan hukumomi, daga cikinsu akwai Ƙaramar hukumar Daura ta jihar Katsina. Katsina City News ta shedi yanda ƙidayar ta gwaji ta kasance bisa Jagorancin Shugaban ƙidayar na ƙasa reshin jihar Katsina Engr. Bala Almu Banye.
ana saran a cikin watan Maris na wannan shekara ne za’a gudanar da ƙidayar a duk faɗin Najeriya inda za a gudanar da ita a tsari zamani ta hanyar na’ura mai ƙwaƙwalwa saɓanin shekarun baya.