Muhammad A. Aliyu @Katsina City News
Ranar Alhamis 26 ga watan Janairu shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bude wasu muhimman Ayyukan raya ƙasa a garin Katsina, wanda Mai girma Gwamnan Katsina Rt.Hon Aminu Bello Masari yayi da suka haɗa da Titin Kurɗe guda biyu na Kofar Kwaya da Kofar Kaura, Ofishin Karbar Haraji na jiha, Gidan Ruwa, da Gyaran Babbar Asibitin jihar Katsina sai Kamfanin Shinkafa na Alhaji Dahiru Barau Mangal.da gini a makarantar koyon fasahar yanayi ta gwamnatin tarayya.da habaka bunkasa watsa ruwan Sha a birnin katsina da babban asibitin katsina da aka daga darajar shi da Kuma Yi masa kwaskwarima
Bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya isa Unguwar Kofar Kaura wanda anan ne ya fara buɗe Titin, sai ya wuce Babbar tashar samar da ruwa dake da nisan akalla mita 400 ko fiye, daga bakin sabon titin a can ma ya bude.
An samu Tankiya a tsakanin Matasan inda bayan shugaba Buhari ya bar wajen suka fito daga sako da Lungunan da aka tsare aka hana wucewa suna cewa “Bamu so, bama yi” wanda ya haifar da Jefe-jefe da Ƙona taya, inda har aka gaggaɓe kankaren Silaf mai ɗauke da Hatimin suna da ranar da Shugaban ya bude wannan Titi.
Katsina City News, sun tattara bayanai ta bakin mazauna Unguwar da masu shagunan kayan sana’a a wajen, wanda suka bayyana mana cewa, “An takurasu an hanasu kasuwanci, sana an hanasu ko leƙawa suga yanda taron ke gudana”
Da muke zantawa da wani a bakin Banki wajen ATM don cirar kudi da ya ki bayyana sunansa yace “Mutane na cikin kunci ka ganni nan tun Asuba nazo na cire kuɗi amma kaga ni-ne na 116, mun shiga halin rayuwa da matsatsi, sana jami’an tsaro sun zo sun takura mana saboda zuwan Shugaban Ƙasa, nema ma ake mu bar bakin Bankin sai shugaban yazo ya tafi.” Yace yana tsammanin hadda wannan ne ya haddasa mutane suka hassala.
Wani kuma cewa yayi lallai ba’aimasu adalci ba saboda matsalar Canza kudi, shiyasa ma kowa ke Allah wadai da shugaban.
Katsina City News ta fahimci mafiya yawa daga masu Allah wadai da ziyarar suna Danganta abin da matsin Canza kuɗi da suke fuskanta.
Shugaban ya samu rakiyar Gwamna Aminu Masari da manyan jami’an Gwamnatinsa.