
Hon. Sani Aliyu Danlami tsohon Kwamishinan Matasa da Wal-walar jama’a kuma ɗan takarar Kujerar Majalisar wakilai ta tarayya a karkashin jam’iyyar APC a mazabar ƙaramar hukumar Katsina ya rabawa Zawuyyoyi Ashirin Tallafin Buhun Fulawa Arba’in da takwas 48 da Shinkafa Buhu Talatin 30 a nan cikin garin Katsina.
Da yake bayyanawa Katsina City News yanda tsarin yake Alhaji Yusuf A.Y yace: dama wannan rabon Tallafi ba bako bane a wajen Hon Danlami, yace ko wace Shekara Idan watan Maulidi ya tsaya yanayin wannan rabon kayan abinci ga Zawuyyoyin Shehinnan Darika, yace kuma duk da ba kowace Zawiyya ta samu Tallafin ba amma anzabi wasu mayan Zawuyyoyi guda Ashirin aka tallafamasu don su rage Hidima. Da muke zantawa da daya daga cikin Shehinnan Darika da suka Samu Tallafin Sheikh Abdulwahab Ladan dake Unguwar Lambobi cikin Katsina, ya bayyana jin dadinsa game da wannan tagomashi da Hon. Danlami keyi, yace “Dama mune ke sanya kudin mu muyiwa Annabi Hidima, sai kuma akace ga wani ko wasu da zasu tallafamaka ka rage wannan hidima, lallai zakaji dadi sosai, kuma yakamata sauran masu hannu da shuni suyi koyi dashi, ba dole sai ‘Yansiyasa ba.” Yace kuma kai dan Siyasa abin saidawa gareka, kuma so kake a siya, don haka kamar Tela ne gwanin iya dinki idan yana so a gane gwanintar sa, ko iyawarsa to zai dinka riga ne mai kyau mai Aiki ya rataye inda za’a gani har ayi sha’awa azo a siya. Don haka Danlami ya gwada Samfur ya rage ga masu bukata su duba Ingancin rigar” inji Sheikh Abdulwahab Ladan.
Zawuyyoyi da suka amfana da kayan abincin sun hada da Zawiyyar Sheikh Abba Abu, Zawiyyar Liman Lawal (Marigayi) Zawiyyar Sheikh Ja’afar, Zawiyyar Sheikh Abdulwahab Ladan, Zawiyyar Shehi Zanguna da sauran su.
Angudanar da rabon Tallafin ne a gidan Hon. Sani Danlami dake Unguwar Modoji Daura da Sabon gidan Gwamnatin jihar Katsina