Tsohuwar ‘yar taƙarar kujerar gwamna karkashin jam’iyyar APC a Jihar Adamawa, Sanata Aisha Dahiru Binani, ta sha alwashin daukaka ƙarar hukuncin kotu da ya soke nasarar da ta samu a zaben fidda gwani na jam’iyyar.
A wata tattaunawa da Binanin ta yi da wata kafar ƴada labarai mai suna Muryar Arewa a jihar, ta ce Nuhu Ribadu kamar dan uwa yake gareta kuma yana da damar ƙalubalantar nasararta a kotu.
Binani ta ce ta dauki hukuncin na kotu a matsayin kaddara saboda a cewarta Allah ne ke ba da mulki ga wanda ya so.
Ta bukaci magoya bayanta da cewa kada su lalata katunansu na zabe saboda hukuncin kotu domin za ta daukaka ƙara.
“A matsayina na kodinetar kwmaitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a jihar Adamawa, zan tabbatar da samun nasararta a zabukan 2023 da ke tafe,” in ji Binani
Idan za a iya tunawa dai, a ranar Juma’a da ta gabata ne wata babbar kotu mai lamba 1 da ke Yola, da mai shari’a Abdulaziz Anka ke jagoranta, ta ayyana soke zaben fidda gwanin gwamna na jam’iyyar APC a jihar ta Adamawa saboda cewa jam’iyyar bata bi ka’idoji da kuma sharuda da aka gindaya mata ba yayin gudanar da zabukan fidda gwani.
Mai shari’a Anka ya kuma gargadi Binani da cewa ta daina daukar kanta a matsayin ‘yar takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar.